A yayin da kasar Amurka ta shirya wani babban taron tattaunawa da shugabannin Afirka a birnin Washignton D.C, sai ga shi wani sabon rahoton bincike da Gallup ya gudanar na nuna cewa, farin jinin fadar White House da majalisar dokokin kasar na ci gaba da raguwa.
Koda yake ba dukkan shugabannin nahiyar aka gayyata ba, bisa wasu dalilai da Amurkar da barwa kanta sani. Masu iya magana dai na cewa, idan ka so uwa to ka so ‘ya’yanta.
A cewar rahoton, kaso 40 cikin 100 na Amurkawa da aka tambaya ne suka nuna amincewa da kimar shugaban Amurka joe Biden, yayin da kashi 55 cikin 100 suka nuna amincewa da yadda yake tafiyar da aikinsa. Tambayar ita ce, wai me ya sa shugabannin Amurka suka gayyaci shugabannin wasu kasashen Afirka a cikin hali da kimarsu ke raguwa? Ruwa dai aka ce ba ya tsami banza.
Bugu da kari, kuri’ar nuna rashin amincewa da Biden ta ci gaba da karuwa, tun watan Satumba shekarar 2021, bayan da sojojin Amurka suka janye daga Afghanistan.
A halin da ake ciki kuma yanzu, yadda Amurkawa ke nuna rashin amincewa da majalisar dokokin kasar, abin babu dadin ji ko kadan, inda kashi 73 cikin 100 na baligai Amukawa ke nuna rashin amincewa da kimar majalisar. Ko da yake tsuntsun da ya jawo ruwa…
An wallafa sakamakon wannan binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’a ne daga ranar 9 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba, wanda Gallup ya gudanar, bayan zaben tsakiyar wa’adi na ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2022.
Sanin kowa ne cewa, duk wani tallafi da Amurka za ta baiwa wata kasa, sai ya samu amincewar majalisun kasar, ga shi kuma sharhin da Gallup ya rubuta na bayyana cewa, majalisar dokokin Amurka za ta fuskanci rabuwar kawuna a cikin shekaru biyu dake tafe, bayan da ‘yan jam’iyyar Republican suka kwace ikon majalisar, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat ke da rinjaye a majalisar dattawa. Don haka, ta yaya Amurka za ta iya agazawa kasashen na Afirka cikin wannan hali na rudani? Koma dai mene ne, yanzu ya rage wa shugabannin Afirka da aka gayyata, su karkade kunnuwansu, don jin sabuwar tatsuniyar da za a fada musu. Dabara kuma ta rage ga mai shiga rijiya. (Ibrahim Yaya)