Connect with us

RIGAR 'YANCI

A Yi Watsi Da Noma A Arewa Idan Babu Tsaro – Giwa

Published

on

An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta kawo karkashen hare-haren da mahara masu dauke da makamai ke kaiwa manoma a yankunan karkara, domin wannan wata dubara ce ta kassara al’ummar arewa, Wakilin gwari-nufe, Alhaji Muhammad Awaisu Giwa ne ya bayyana hakan safiyar lahadin makon da ya kare a minna.

Alhaji Awaisu Giwa, yace gwamnati na yekuwar a koma gona wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddadawa a bayanin da ya yiwa ‘yan kasa amma a na yi shirin zagon kasa wanda hakan ba zai haifarwa yankin nan da mai ido ba idan aka cigaba da wannan yanayin da aka hanawa mutanen karkara zama a gidajen su ba, shin wa ake son yayi noman masu hannu da shuni ko ita gwamnatin ne zasu iya noma karkarun da ake watsawa, wannan ba abu mai anfani ba.

Abinda ke baiwa kowa mamaki shugaban kasar nan dan arewa ne, kuma talakawa sun zabe shi ne dan tunanin shi ne zai iya ceto yankin nan daga halin da ta ke ciki amma a wayi gari a ce ba inda ake daidaitawa sai arewa, har yanzu ban ji wani bayarbe ko inyamuri da aka hanawa zama gidansa ta hanyar kisa ba sai a al’ummar arewa, shin wannan me yake nufi ne, idan shugabannin tsaron kasar sun kasa ne a kau da su a kawo wadanda za su iya mana, wannan abin kunya ne da takaici a ce dan yankin ku na shugabanci kuma ya kasa magance maku matsalolin da ke damun ku, yau a cikin gidansa ma mutane ba su tsira kusan duk yankunan da suka shahara da noma kuma suka bada gudunmawa wajen inganta tattalin arzikin kasar nan wato jihar katsina kusan a kullun sai an salwantar da rayukan jama’ar karkara manoma, a satin da ke karewa kowa ya ga abinda ke faruwa a kananan hukumomin Dandume, Funtua da Faskari wanda su din ne ke gangaro mana jihar Neja. Ya kamata gwamnatin tarayya ta sakarwa gwamnatocin jahohi mara su dauki matsalar tsaro a hannun su domin gwamnatin tarayya ta kasa, kai ke da jami’an ‘yan sanda da na soja, kai ke da jami’an tsaron farin kaya amma wankin hula ya kai ka dare. Ta ina za a ce ‘yan sanda dubu talatin da bakwai ne zasu iya tabbatar da tsaro a kasar nan, ko mu jihar Neja da ke da kananan hukumomi ashirin da biyar ‘yan sanda dubu talatin da biyar zuwa da bakwai in har aikin kirki zasu yi ba zasu wadace ma ba.

Maganar gaskiya in har da gaske gwamnatin tarayya ke yi kan inganta harkar noma a kasar nan to ba ta shirya ba, kawai wasa ake da hankulan jama’a, domin ba yadda za a iya yin noman nan a irin wannan halin da muke ciki na rashin tsaro, domin manoman an hana masu zama a gidajen su, an koma a na kashe su da daidai kuma a na garkuwa da wasu.

Ya kamata shugabanni musamman makusantar shugaban kasa su tada dogon barcin da yake yi arewa kan a na gab da kammala ta cikin hikima.

Amma zai yi wu a ce a kasar cikin jahohi talatin da shida muke da jahohi goma sha tara mu zuba ido a cigaba da wannan halin na rashin kishin kasa ta hanyar zubar da jinin jama’a kuma mu rufe bakunan nan mu muna kallo ba kuma sannan a ce wai muna kishin arewar, wanda bai yi kishin gidansa ba to gidan wa zai iya kishin.

Yana da kyau a yiwa tufkar hanci domin gano inda matsalar ta ke, ina jin tsoron ranar da talakan arewa zai yi fushi domin ba zai haifar da da mai ido ba. Inda man suke so to gwamnati ta ba su kayan su tunda sun ce na su ne amma a daina zubar da jinin talaka da bai ci ba, bai sha a banza domin wannan kasawa ce ta shugabancin jagororin mu.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: