Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sabbin naɗe-naɗe da yi wa wasu jami’an gwamnatinsa sauyin guraben aiki domin inganta shugabanci da samar da kyakkyawan aiki a jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta jaddada jajircewar gwamnan wajen tabbatar da gaskiya, amana, da ƙwarewa a sha’anin mulki.
- Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar
- An Watsa Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Karon Farko A Najeriya
Jamila Magaji Abdullahi ta zama sabuwar Akanta-Janar ta Jihar Kano.
Tana da ƙwarewar aiki ta sama da shekaru 16 a fannin harkar kuɗi, kasafin kuɗi, da sauransu.
Kafin naɗin nata, ta kasance Darakta a Ma’aikatar Kuɗi ta Jihar Kano.
Haka kuma, gwmanan ya naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta a ma’aikatar kuɗi.
Liman yana da ƙwarewa a fannin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen inganta tsarin kuɗi na jihar.
Gwamnan ya kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa.
Aikinsa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu.
Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa shi a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA).
An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara.
Haka kuma, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri ta Jihar Kano (Kano Line).
Sa’idu Abdullahi Shu’aibu zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba kuma Muƙaddashin Manajan Darakta, inda za su duba tare da tsara ayyukan Kano Line cikin watanni shida masu zuwa.
Gwamna Abba ya yi kira ga dukkanin sabbin jami’an da aka naɗa da su jajirce tare da nuna ƙwarewa, amana, da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.
Ya sake jaddada muhimmancin rawar da za su taka wajen ci gaban Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp