Bello Hamza" />

Abin Da Ya Kamata Mu Kiyaye A Lokacin Damuna

A irin wannan lokacin na damuna da muke ciki;ya zamanto wajibi gare mu mu yi la’akari tare da kula da caccanzawar yanayi domin tsira da lafiyarmu.Domin kamar yadda lokacin sanyi da na zafi ke da khususiyyarsu,haka ma lokacin damuna yake da na shi kebantattun yanayiyyikan da yake zuwa da shi.Ga kadan daga abubuwan da suke faruwa a wannan lokacin:
1.Yawaitar Zazzabin Maleriya Da Taifod:Tabbas a wannan lokacin ana yawan samun wadannan lalurorin a cikin al’umma.Mafiya yawan lokuta a yayin da zazzabin Maleriya ya shiga gida, za ka ga a hankali a hankali sai ya shafi kowa a gidan kafin ya fita.Yau za ka ga Mahaifiya ba ta da lafiya,gobe kuma ka ga Mahaifi ya kamu,da zaran ya warke kuma kwatsam sai ka ga ya damki ‘ya’yan gida yana yin wuji-wuji da lafiyarsu.
A nan ya zamanto wajibi ga iyaye su yi matukar kulawa da ruwan da ‘ya’yansu da su kansu za su sha a duk sadda za su sha ruwa,a tabbatar da ce wa mai tsafta ne wanda bai gurbata da datti ba.
2.barkewar Annobar Mura:Ana yawan samun yaduwar mura a lokacin damuna a sakamakon sanyin da yake biyo bayan daukewar ruwan sama.A nan ya zamanto wajibi ga iyaye su kula da sanyawa yaransu kayan sanyi a duk sadda aka fuskanci akwai sanyi din.Sannan su ma su yi matukar kula da kawunansu domin tsira da lafiyarsu.
A gefe guda kuma,ga wanda ya kamu da cutar mura,a gare shi ya yi matukar kulawa wajen rufe hancinsa a sadda zai yi atishawa,haka ya yi matukar kulawa da wuraren da zai rika zubar da yawunsa ko majinarsa gudun ka da ya rika yadawa mutane cutar.
3. Kashe Wuta Bayan An Kammala Girki:Mafiya yawan mata musamman a karkara su na amfani da Itace ne wajen dafa abinci.To yana da gayar muhimmanci a yi matukar kulawa da kashe itace ko garwashin da aka yi aiki da shi domin gujewa ruruwar wutar daga baya.A irin wannan lokaci a kan samu tasowar iska mai karfi a yayin da za a yi ruwan sama,rashin kashe wutar da aka yi amfani da ita,zai iya haddasa tashin wutar da za ta haifar da gagarumar matsala a cikin gida.
4. Tsaftace Kwanukan Cin Abinci: barkewar annobar Kwalara a birane da kauyuka na yawan yaduwa ne a lokacin damuna.Yana da gayar muhimmanci a kula da tsaftar ruwan da za a dafa abinci da shi,haka a kula da wanke kwanukan da ake cin abinci da su,ka da a yi saken hakan,domin samun kariya daga annobar kwalara.
5. Matsalar Ciwon Ido: Galiban a lokacin damuna an fi samun barkewar annobar ciwon ido.A nan a duk sadda mutum ya ji idanuwansa na masa ciwo,ya kiyaye sosawa da hannunwansa,ya kamata ne ya je wajen kwararren likita ya bayyana masa damuwarsa,tare da daukar matakan da ya dora shi na magani da sauransu.
6.Yashe Magudanan Ruwa:
A lokacin damuna ana samun ambaliyar ruwa daga lokaci zuwa lokaci.Mafiya yawan lokaci kuma ruwan yana yiwa kan shi hanya ne saboda ba a tanadar masa hanyar da zai bi ba a yayin da aka yi shi.A nan ya kamata a yi matukar kulawa da yashe magudan ruwa da gasken-gaske domin da zaran an yi ruwan sama,ya samu damar sauka tare da bi ta cikin shi.
7.Tsaftar Makewayi: A lokacin damuna a kan samu cututtuka kala-kala masu yawa wadanda kudaje da sauran kwaruka suke yadawa.Yana da gayar muhimmanci a rika tsaftace Makewayi tare wanke shi da aizal da sauran sibadaran kashe kwayoyin cuta.Haka a duk sadda aka fito daga Makewayi,a wanke hannu da sabulu kafin a taba wani abu da ake amfani da shi.
8. Shiga Gidan Sauro A Yayin Da Za A Barci: Tabbas sauro yana cin karensa babu babbaka a lokacin Damuna.A nan akwai bukatuwar a duk sadda za a kwanta barci,a yi kokarin shiga gidan sauro domin samun kariya daga cizonsa da cutarwarsa.Bugu da kari a rika yin amfani da magungunansa masu inganci domin tsira daga sharrinsa.
9. Kula Da Tsaftar Gida:Tsaftar gida tana da gayar muhimmanci a lokacin damuna.Domin a lokacin kwayoyin cututtuka suke yaduwa tare da kama gangar jikin mutane.Yana da gayar kyau a rika tsafta ce gida ta hanyar share shi akai-aka.
A gefe guda kuma,ko ba komai tsafta wani muhimmanin lamari da addinan Musulumci da Kirista suka muhimmantar da ita a cikin tsarkakan littafansu.Saboda haka kula da tsafta muhimmin abu ne.
10. Kula Da Gine-Ginen Da Suke kokarin Rushewa: A yayin da lokacin damuna ya kewayo,ana yawan samun rushewar gine-gine musamman a karkara.A nan ya kamata ga iyaye maza su rika gyara gidajensu tun kafin lokacin damuna.Amma idan ba a samu damar hakan ba,ya kamata ayi gaggawar gyara dakunan da ake da tabbatacin su na da matsala domin gujewa matsalar rushewar dakuna a kan mutane.
11. Adana Kayan Noma A Lokacin Kaka:Yana da kyau ga kananan Manoma wadanda suke noma iya abunda za su ci kawai,su yi kokarin adana kayan noman na su domin amfana da su a watanni masu zuwa.Mafiya yawan lokuta kananan Manofa da zaran sun samu amfanin gona,sai su sayar da su bisa farashi mai sauki,bayan wani lokaci kuma,sai kayan noman da suka sayar su yi tsada fiye da yadda suka sayar har ma su gagare su saya.
12. Hana Yara Yin Wanka A Cikin Ruwan Sama: Galiban a yayin da ake ruwan sama,akan samu yara na fita domin yin wanka a ruwan da ke sauka daga sama.Yin wankan kuma yana haifarwa da yaran kamuwa da zazzabi da mura.A nan ya kamata iyaye su nuna matukar kulawa a kan yaransu tare da killace su a daki a sadda ruwan sama ke sauka.
Allah ya bamu damuna mai albarka.

Exit mobile version