Abin Da Ya Sa Gwamnati Ke Ci Gaba Da Cin Bashi – Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattijai

Daga sulaiman Ibrahim,

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da karbar lamuni domin samar da ababen more rayuwa, har sai hukumomin da ke samar da kudaden shiga sun zama yadda ake tsammaninsu.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a jawabin da ya gabatar a farkon zaman majalisar na maraba da dawowar sanatoci daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ya ce yanzu gwamnati na matukar bukatar karin kudaden shiga, domin baiwa gwamnatin damar cigaba da ayyukan raya ababen more rayuwa.

Exit mobile version