A kwanan baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta samar da wuraren kiwo 368 a Jihohi 25.
Wannan yunkurin dai, manoma da dama da ke a cikin kasar nan, sun bayyana hakan a matsayin matakin da ya dace, inda suka sanar da cewa, matakin zai kuma taimaka matuka wajen rage yawan ricikin da ke aukuwa a tsakanin wasu manoma da makiyaya da ke a fadin kasar nan.
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
- Kudin Da NNPC Ke Kashewa A Tallafin Mai Ya Wuce Kima – Hamid Ali
Hakan ya sanya wasu daga cikin jihohin kasar, sun bayar da hadin kai domin a cimma wannan nasarar da gwamnatin tarayya ta sa a gaba.
Matakin na Buhari ya dauka ya biyo bayan shawarwari ne da wani kwamiti na musamman ya ba shi, wanda ya yi nuni da cewa, samun wuraren kiwo zai taimaka wajen rage rikicin manoma da makiyaya da aka gaza kawo karshen hakan a kasar nan.
Da yake yin tsokaci kan matakin Shugaban kungiyar manoma ta kasa Kabir Ibrahim ya ce idan aka samu irin wanan gagarumin sauyi, ya kamata mutanen kasar nan su yi na’am da shi, musamman ganin cewa, tsarin zai taimaka wajen kara habaka yin noma kasar nan.
A cewar shugaban, jihohin Arewa da jihohin Kudu duk daya ake, ba abin da ya bambanta kasar sai ra’ayi, kuma bai kamata a bari ra’ayoyi su raba kan kasar ba, inda ya yi nuni da cewa, ya kamata a hade wuri guda a yi wa kasa aiki da zai kawo ci gaba.
Har ila yau, an ruwaito wani dan majalisar gudanarwa ta hukumar tantance ingantaccen iri na kasa Ibrahim Musa ya ce wannan abu ne da ake da shi a kasa tuntuni, kuma in an mayar da shi yanzu yana da kyau.
A cewarsa, wadannan wuraren kiwon dama tun 1948 ake da su har zamanin su marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato an yi amfani da su a Jihohin kasar.
Ya sanar da cewa, yunkuri ne mai kyau wanda zai taimaka wajen tattara kan makiyaya a wuri guda, domin a tsugunad da su domin ba yadda za a a yi manomi ya rayu babu makiyayi yana mai cewa makiyayi ba zai rayu ba sai da manomi.
Kabiru ya sanar da cewa, yin hakan zai sa a samu abubuwan more rayuwa cikin sauki har a samu kudaden shiga sosai domin zai taimaka wa tattalin arzikin Nijeriya.
Ya bayyana cewa, ya zama wajibi manoma da makiyaya su sani cewa wannan yunkuri shi ne babban abin alheri ga al’umman kasa da kuma jummar da gwamnatin tarayya take da shi a kara bunkasa fannin aikin noma a kasar nan.
Ya ce idan aka samu dama aka kirkiri wannan shiri na Rugga, zai kawo ci gaba sosai na samun tagomashi irin su makarantu da hanyoyin kiwon lafiya da ruwan sha musamman ga makiyaya.
Ya kara da cewa, zai kara samar da hanyoyin samar da da sana’a ga ‘yan Nijeriya, inda ya yi fatan za a gudanar da aikin a cikin fahimta.
Amma abin taikaici, wasu jihar Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma, har da wasu a Arewa irin su Jihar Binuwai sun fito fili sun kasance ba su goyin bayan wannan yunkurin na gwamnatin tarayya ba.
samu amfanin gona wanda an jima ba a samu irinsa ba saboda albarkar damina. Duk da matsin rayuwa a Nijeriya a yau, akwai magunguna da sauran muhimman abubuwan rayuwa da mutane za su saya ba kamar a Benezuela ba.
Wannan bambanci tsakanin kasar biyu wajen tasirin faduwar farashin man fetur a kan rayuwar jama’a ya samo asali ne daga yayin da tattalin arzikin Benezuela da mutanen ta suka dogara kacokam a kan man fetur domin samun kudaden shiga da abinci da sauran muhimman abubuwan more rayuwa daga kasashen.