ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

by Idris Aliyu Daudawa
7 months ago
Ilimi

Nau’ukan Ilimi

Ilimin da mutum yake samu a makaranta, wanda ake samu ba a makaranta ba,wanda ya bambanta da kuma wanda ya bambanta da nau’ukan ilimi biyu.

Tsarin ilimin da sai an je makaranta

ADVERTISEMENT

Irin wannan nau’in ilimin yana da alaka da zuwa makaranta ayi karatu ta hanyar yin amfani tsarin koyarwa na yanayin cikin aji na makaranta.Tarihi ya nuna masu arziki wato kudi sune ke da hanyar littattafan makaranta da kuma yadda,za a,ware lokaci wanda za’a karanta da kuma koyo. Juyin juye hali na harkar masana’antu da yadda al’ummomi suka sauya yasa aka maida hankali kan neman ilimi. Iyalan mutane masu matsakaitan halin rayuwa sua ga ya dace su nemi ilimi. (Lumen, n.d.)

Yanzu mutane da yawa ne ake sa ran za su samu ilimi wanda yake mafi karanci,wanda ya fara daga makarantar elimantare.Dalibai su kan bi hanyoyin da za su koyi karatu domin su samu ilimi ta hanyar kwararru masu koyarwa,da shi tsarin yadda za a koyar da su, har ma da gwada su da ake yi ta jarabawa,domin tabbatar da sun koyi gwargwardon abubuwan da ake bukata su koya.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

 

Tsarin ilimin da ba sai an je makaranta ba

Irin wannan nau’in ilmin shi ba tsara shi ake yi ba, hakanan ma ba yana bin wani abinda aka shirya bane dangane da koyarwar. Irin wannan ilimin baya bukatar wani adoI wato ilimin da a ciukin ajin dake makaranta ake koyon shi ba. A waje n eake koyon shi wato manufa ba a wata makaranta ba wadda ake koyarwa domin a samu shi ilimin. Wannan kuma yana faruwa ne idan mutane suka samu karuwa da wasu dabaru ko ilimi daga gida, dakin karatu, ko kum wata kafar sadarwa ta na’urar waya da duk wani abinda za’a iya amfani da shi domin hakan.Bugu da kari irin wannan ilimin ana iya samun shi daga wurin Shugabannin al’umma.

Kasancewa cikn al’umma ta wannan hanya ko waccan irin hakan ma wata hanya ce da mutum yake karuwa da nau’in ilimin da ba sai an je makaranta ba an zauna, a aji. Irin wadancan Malaman ai Iyaye ne, ‘yan’uwa, da kuma makwabta, da wasu al’umma wadanda su sun koya ne daga irin dabarun da suka koya a rayuwa,daga iri yadda mutum zai sa kaya/sutura da anau’oin Bukukuwa ko wasu raturruka, yadda za a sayo abubuwan hadawa ayi abinci,da kuma yadda za’a lura da tsaftar jiki.

Sai dai kuma akwai wasu abubuwan da suke nasaba da yadda al’adu suke yaduwa,yayin da abin kan faru ta wani yanayin da ba ayi tsammani ba,yana iya kasancewa irin ilimin a ake karuwa da shi ba sai an je makaranta ba.Ya dangata ko dogara da yadda al’umma suke tafiyar da al’adunsu,yadda suke yi na’am da su,da kuma yadda halayen zamantakewa suke.

 

Ilimin da ya hada da nau’oin ilimi biyu

Shi iri wannan nau’in ilimin ya sha bamban da guda biyun domin abin ya danganta ne da irin salon da yake tafe da ita koyarwar ta kunsa.Shi yana da irin na shi tsarin kai tsaye kuma,amma shi ma ba a makaranta ba ake iya koyon shi ba.Akwai tsarin yadda yake wanda ba mai rikitarwa ba,babu kuma wani lamarin kayyade shekaru.

Alal misali akwai irin wuraren da ake koyon shi wadanda suka bambanta da guda biyun, koyon sana’oi wuraren da ake koyar da su, tsarin horarwa mai gajeren zango,irin na Shugabannin Kamfanoni wadanda ba wai sai kwararru ba wadanda suka samu ilimin ta irin nau’in ilimin da ake koyar da shi a cikin aji.

 

Me yasa ilimi yake da muhimmanci?

Me yasa ilimi yake da muhimmanci?Ilimi yana da muhimmanci saboda dalilai masu yawa. Ta hanyar ilimi mutane/ al’umma suna koyon yadda za suyi karatu, rubutu, da kuma saurare. Gaba daya lamarin ilim har ya kunshi rayuwar abubuwan da mutum yake son cimmawa a gaba.Mutanen da suke da ilimi mai zurfi irin sune ake rubibinsu a wuraren da ake daukar ma’aikata inda kuma albashinsu ya kan kasance mai tsoka. (Abulencia, 2021) Hakananma shi ilimi yana maganin fatara, da yunwa, inda yake bada damar yadda mutum zai samu ci gaba. Irin hakan ce ta sa Iyaye suke kokarin sai ‘ya’yansu sun je makaranta, yayin da ita kuma gwamnati take taimakawa ta hanyoyin da za su sa dukkanin yara da manya sun samu da karuwa da ilimin. (UNESCO, 2011)

Bayan haka ma ilimi yana taimakawa ‘yanmata da mata wajen samun dama wadda ba za a samu rata mai yaw aba tsakaninsu da maza.Ta haka ne aka samu rage yawan yaran mata kanana ke daukar ciki da kashi 6 cikin 100, saboda karun shekarun da ‘ya’ya mata suke yi wajen karatu kamar yadda Bankin duniya ya bayyana.Ita ma Hukumar dake karkashin majalisar dinkin duniya da ake kira UNESCO,mai kula da lamurran ilimi, kimiyya, da kuma al’adu ta gano cewa jaririn da mahaifiyarsa ta iya karatu yana kashi 50 na yiyuwar samun damar kaiwa har zuwa shekara biyar,wannan ya nuna ilimi ya taimaka wajen irin yadda kananan yara suke mutuwa kafin su kai shekara biyar.

Sai dai kuma wani nazarin da aka yi ya nuna an samu koma- baya wajen samun amsar tambayar me yasa ilimi yake da muhimmanci ga samun nasara? A wani rubutu mai taken “Amfanin abokantaka /’yan’uwantaka tsakanin ilimi da tattalin arziki,halayya da kuma matsayin abin a siyasance wanda”International Journal of Social and Management Studies,Deak and Tanama ya wallafa, a shekarar(2021)ya bayyana cewa “Idan aka samu matsalar rashin yin shiri da tsarin ilimi wanda ya kamata yana sanadiyar haifar da manyan matsalolin da suke da amfani idan tun farko an yi su saboda kaucewa aukuwar irin hakan: rashin aikin yi,aikata laifuka,shan muggan kwayoyi,idan ana maganar ci gaban gwamati ne ta bangaren tattalin arziki,a hanyoyi da dama hakan ya ta’allaka ne kan taimakon da take samu daga kimiyya da kuma fasaha.’’Don haka shi yasa ilimi yake da amfani/ muhimmanci ga ko wadanne al’umma,da daidaikun mutane’’.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ilimi

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

November 30, 2025
Next Post
Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida - Yahaya Yakubu

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.