Rahoton hadaka da hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya (FAO) da hukumar kula da kasuwanci ta duniya (WTO) suka fitar sun bayyana cewa, manoma a Nijeriya za su ci gaba da fuskantar karancin takin zamani Iadan Allah ya kai mu badi wato shekara ta 2023.
Hukumomin biyu sun sanar da hakan ne a rahoton hasashe na shekarar 2023, inda suka bayyana cewa, mai yiwa a samu karancin takin na zamani daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2023, inda suka bayyana cewa, hakan zai iya janyo karancin abinci a kasar nan.
- Muna Ci Gaba Da Kokarin Ceto Sojar Da Aka Sace – Sojoji
- Sharhi:Al’ummar Kasar Sin Na Sa Ran Rungumar Sabuwar Rayuwa Cikin Sabuwar Shekara
A cewar hukumomin, tsadar takin zamanin, zai janyo karancinsa a kasar nan.
Hukumin sun bayyana cewa, nahiyar Afirka ta kasance daya tilo a tsakanin kasashen da ke cikin nahiyar da ke samar da takin zamani daga kashi 3 zuwa 4 daga cikin dari.
Sai dai, abin takaici, duk da kasancewar Nijeriya na da kasar noma mai kyau, amma ana ci gaba da fusakanatar karancin abinci a kasar.
Karancin takin zamanin zai kawo matsaloli da yawa a bangaren noma a kasar nan.
Rahotin ya kuma bayyana cewa, tashin farashin dalar Amurka, musamman wajen yin amfani da ita a hada-hadar kasuwanci da kuma yakin da ake ci gaba da yi, a tsakanin kasashen Rasaha da Ukraine, haaakan zai kara haifar da matsalar safarar takin na zamani zuwa kasuwannin duniya.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan cewa, wasu kasashen da ke cikin Afirka za su fuskanaci karancin takin zamani bana.