A jiya ne fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta iya ruwan bama-bamai a dajin da aka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, inda ta ce yin hakan zai kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, laifinsu kadai shi ne hawa jirgin kasa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da yake maida martani kan wani sabon faifan bidiyo da ‘yan ta’addan jirgin kasan suka fitar, inda suka yi barazanar kashe wasu daga cikin fasinjojin tare da yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i idan ba a gaggauta biya musu bukatunsu ba.
A cikin sanarwar, Garba Shehu ya ce jami’an tsaro na kasar nan ba ragwaye ba ne, amma ‘yan ta’addan na kokarin amfani da farfaganda ne don tilasta wa gwamnati su amince su mika wuya ga bukatunsu na siyasa – wannan dabaru ne wadanda an saba ganin su a duk fadin duniya.
A cewarsa, jami’an tsaro na da tsare-tsare da dabarunsu wajen yaki da ta’addanci wadanda ba zai yiwu a dinga nuna su a kafafen yada labarai ba.
Shehu ya kara da cewa yin amfani da sojojin sama wajen tayar da bama-bamai a Dajin da ‘yan ta’addan suke, zai halaka mutanen da gwamnati da ‘yan Nijeriya ke son ceto wa da ransu.