Wani fashewa da ake zargin daga abubuwan fashewa ne da wani mai hakar zinariya ya ajiye a Sabon Pegi, ƙaramar hukumar Mashegu a Jihar Neja, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkatar mutane shida a ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa Yushau, wani mai haƙar haƙar zinariya, ya ajiye abubuwan fashewar ne a gida kafin su tashi yayin da ake shirya su don kai wa wuraren haƙar ma’adinai a yankin. Fashewar ta shafi gidaje da dama tare da lalata dukiyoyi.
- Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta’adda Masu Yawa A Neja
- Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta
Kakakin Rundunar ’Yansanda ta Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar Fatima Sadauki tare da jikkatar wasu mutane shida da aka kai Asibitin Kainji domin jinya. Haka kuma, gidaje 12 sun lalace sakamakon fashewar.
Kakakin ya ƙara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya umurci a gudanar da bincike tare da tura tawaga ta cire abubuwan fashewa (EOD-CBRN) zuwa wurin domin bincike na musamman. Ya kuma bayyana cewa wanda ya ajiye abubuwan fashewar, Yushau tuni ya tsere, amma an tabbatar da zaman lafiya a yankin yayin da ake ci gaba da sa ido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp