Akwai nau’ikan abinci da ya kamata a ce ko wacce mace ta ba da muhimmanci wajen kokarin ci domin hakan zai kara mata lafiyar jiki da kuma dorewar ni’ima a jiki domin karin danko zama a gidajen aure.
A na son mace ta dinga cin daya daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin karfi ko rashin halin maigida, za ki iya mallakarsa, kuma wadannan abubuwa suna kara lafiya da kuzari a jikin dan’Adam, kuma cin irin wadannan nau’ikan abinci suna kasancewa garkuwa ne ga kamuwa da wasu cututtuka haka kuma ya na karawa mata ni”ima a zamantakewar aure.
- Ku Daina Zagin ‘Yan Fim Domin Muma Iyaye Ne Kuma Muna Da ‘Ya’ya – Mai Sana’a
- Abubuwan Da Mace Mai Ciki Ya Kamata Ta Sani
Wadannan cima su ne kamar haka:
Kankana, Ayaba, Gwanda, Goba, Lemu, Tumatir, Rake, Aya, Kwakwa, Dafaffiyar gyada, Zuma, Nono, Madarar Shanu, Gurji, Dabino, Chukwi, Zogale, Ruman, Inibi, Tuffa, Zaitun.
Daga yadda aka lissafo wadannan kayan marmari a jere ya kamata uwargida ta sani cewar abubuwa ne masu saukin samu sannan kuma masu saukin sarrafawa, da kudi kalilan uwargida za ta iya mallakar wadannan abubuwa.
Kowa dai ya san cewa mace sai da gyara, a kalla ya kamata a ce ko ba kullum ba ko a sati sau daya uwargida ta samu daya daga cikin wadannan abubuwa ta ci. Yawancin wadannan nau’ikan abinci ba ni’ima kadai ba har fatar jiki suna taimakawa wajen gyara ta.