Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin wata mai alfarma na Ramadan a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.
Watan Azumi lokaci ne da musulmi ke kaurace wa abinci tun kafin ketowar alfijir har zuwa faduwar rana. Hakan yake sa mutane jin yunwa da gishin ruwa. Masu Azumi sukan ci abinci daban-daban a lokacin sahur da na buda baki.
- “Tutar Dimokuradiyya” Da Kasar Amurka Ta Rike Ta Lalace
- Tsaron Iyakoki: ACG James Sunday Ya Jagoranci Taron Samar Da Dabarun Aiki A Jos
Sai dai likitoci sun bayyana nau’in abincin da ya kamata mai Azumi ya ci da wanda ya kamata ya kauracewa.
Dakta Lawan Musa Tahir, wani likita a asibitin Nizamiye da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, ya shaida wa BBC Hausa irin abincin da ya kamata masu Azumi su ci da kuma wadanda ba su kamata ba.
Wanne nau’in abinci ya kamata mai Azumi ya ci?
Masu fama da wasu cututtuka
Masu Azumi sun kasu kashi-kashi: misali, akwai wanda da ma kafin Azumin saboda da wata larura a asibiti za a dora shi kan abincin da ya kamata ya ci ko kada ya ci.
Misali a nan shi kamar wanda yake da ciwon suga za a dora shi kan dokoki na yanayin abincin da zai ci, ko wanda yake da ciwon hanta, shi ma za a dora shi kan dokoki na abinci da zai ci, sai mai olsa shi ma akwai abubuwan da ya kamata ya ci da kuma wanda bai kamata ba.
Haka kuma wanda yake da ‘food allergy’, wato wanda jikinsa ba ya karbar wasu nau’o’in na abinci: To, kun ga wannan tun kafin Azumi akwai dokoki na yanayin abincin da yake ci, don haka idan Azumi ya zo zai ci gaba da bin dokokin.
Mutanen da suke koshin lafiya
Sai kuma mutanen da su da ma lafiyarsu kalau, su ma ya danganta da inda suka samu kansu lokacin Azumi.
Misali, idan mutum yana zaune a irin kasashenmu masu zafi inda mutane suke bukatar yawan shan ruwa a kai – a kai, su ma akwai yadda ya kamata su yi. Ga jerin abinci da abubuwan da suka kamata masu Azumi su yi:
Guji cin abinci mai yaji da wanda yake da maiko sosai saboda zai kara musu kishirwa sannan akwai zafin gari. A ci abinci mai ruwa-ruwa, musamman ‘ya’yan itatuwa irin su Ayaba, Abarba, Gwanda, Kankana da makamantansu
A sha ruwan zafi kamar shayi ko koko ko kunu domin suna gyara ciki musamman bayan an dade ba a ci abinci ba. A guji cika ciki fal da abinci za ka ga wasu suna cin abinci sosai idan an sha ruwa. Hakan yana da matsala. An fi so ka ci abinci kadan sannan ka huta yadda idan an jima za ka iya sake ci.
A guji shan taba da dangoginta saboda tana da illa. Babu laifi idan an motsa jiki lokacin Azumi amma a yi shi saisa-saisa.