Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna
TARIHIN ABUBAKAR ABUBAKAR ZANGO
An haifi Abubakar Abubakar Zango a Garin Zango Kataf da ke cikin Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Mayu, 1980. Ya yi karatunsa na firamare a Kaduna Capital School, sannan ya wuce Kwalejin tunawa da Sardauna, wato Sardauna Memorial College Kaduna. Daga bisani ya wuce kwalejin kimiya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke kaduna, wato Kaduna Polytechnic.
YADDA AKAYI YA TSINCI KANSA A HARKAR PRINTING
Ni dai na taso a matsayin dan gata a gidanmu, saboda duk wani rufin asiri na rayuwa da mutum ke nema Allah ya bamu, akalla akwai ma’aikata masu yi mana hidima kusan mutum 10 a gidanmu, domin mahaifinmu mutum ne wanda bai yarda da duk wani uziri na rashin karatu ba. Wannan dalili ne ya sanya duk cikinmu babu wanda ba shi da mai yi masa hidima, kamar wanki, shara da dai sauran aikace-aikace irin na gida.
Amma duk da irin wannan gata da nake da shi bai hanani zuwa domin neman na kaina ba. Saboda zan iya tunawa da wata rana ina zaune muna hira da wani abokin mahaifina kuma mai gidana, Alhaji Yusuf Dambo Kangiwa, wanda shi ne shugaban kamfanin buga takardu na Kangiwa Press. Ya ce mun Abubakar, ko za ka iya aikin buga takardu? Na ce masa kwarai da gaske kuwa, ya ce mun aikin akwai wahala fa, amma na ce masa zan iya jure duk wata wahala.
Cikin ikon Allah daga farko na sha wahala sosai, saboda na farko ban iya aikin ba, domin ba abin da na karanta a makaranta kenan ba. Sannan an hadani aiki da wadanda ba sa jin yarena kuma ba al’adarmu daya ba. A kullum ba su da wani aikin da ya wuce su yi ta mun dariya suna yin gulma ta da yarensu, akan cewar ni ban saba da wahala ba, da wuya na jure wahalar. Amma cikin ikon Allah ban dauki tsawon lokaci ba sai da na fahimci yadda aikin yake sosai, kuma har na fi wasu wanda na zo na tarar a wajen iya aikin sosai.
GWAGWARMAYAR DA YA YI
Na fara aikin buga takardu cikin wahala sosai, saboda ni dai na taso a gidanmu ban san menene ye yunwa ba, ban san wahalar rashin kudi ba, sannan idan har ka ga na yi tafiya mai tsawo a kafa, to filin kwallo zan je; duk inda za mu je a mota ake kai mu. Amma a dalilin aikin koyon buga takardu, na san menene wahala, sannan na horu da yunwa, domin idan na cin abinci da safe a gidanmu na fita zuwa wurin aiki, to ba ni zan kara cin wani abinci ba har sai dai har idan na dawo gida da daddare. Ba zan iya kirga maka ko sau nawa na taka a kafa tun daga gidanmu har zuwa cikin gari wajen koyon aiki ba.
Gaskiya na sha wahala sosai, hatta yan gidanmu dariya suke mun, domin a lokacin kowa ya zura ido yana jiran ya ga gazawata, hatta abokaina dariya suke mun, sun dauke ni a matsayin wawa wahallale, saboda suna mun kallon wanda ya fito gidan gata amma ya mai da kansa mai bauta. Amma yanzu Alhamdulillah, tun da ni ma mai gidan kaina ne, domin yau kusan shekaru 5 kenan da na mallaki nawa kamfanin mai suna Baban Saude Printing Press. Sannan zuwa yanzu na yaye sama da mutum 25, wanda suka koyi aikin buga takardu a karkashina. Sannan yanzu haka akwai mutum 15 dake aiki a karkashina. Ka ga kenan babu abin da zance wa Ubangiji, sai dai godiya.
YANAYIN HARKAR BUGA TAKARDU A YANZU
Gaskiya akwai bambanci tsakanin lokutan baya da yanzu. Na farko, a lokutan baya babu yawan gasa a aikin, sannan a lokutan baya babu masu aikin printing din da yawa kamar yanzu. Saboda zan iya tunawa a lokutan baya idan aka kawo mana aiki kamfaninmu, idan aikin ya fi karfinmu sai mun tura zuwa Lagas, domin a lokutan baya ko katin aure za a buga sai an je Legas, sannan kayayyakin aikin ba su yi tsada kamar yanzu ba. Amma yanzu kam sai dai hamdala akwai, saboda aikin buga takatdu ya zama ruwan dare game duniya, zamani ya kawo mana ci gaba sosai, domin komai ya koma komfuta, hatta katin gayyata na aure an rage bugawa, ba a maganar kalandar biki yanzu, domin a wajen wasu ya zama kauyanci.
KALUBALEN DA MAI AIKIN PRINTING KE FUSKANTA
Babban kalubalen da matune masi irin sana’armu ke fuskanta shi ne hatsarin buga takardun boge ba tare da izini a hukumance ba. Saboda aikinmu aikin sirri ne sosai, duk mai aikin printing ya san irin dokokin da ke bisa wuyansa na yin aiki kafada da kafada da jami’an tsaro. Domin duk mutumin da ya kawo maka aikin buga takardun makaranta, ko sabunta takardun mota, ko katin shaidar aiki (ID Card), to, ya zama wajibi a garemu mu bukaci a kawo mana shaidar izini a rubuce daga hukuma, kafin mu amince a buga masa. Domin wani lokaci dan karamin aikin da ka raina shi ke janyo maka matsala. Amma ni dai Alhamdulillah, yau kusan tsawon shekaru goma 12 kenan ina wannan aikin, amma babu wani abu da ya taba hadani da hukuma akan saba dokar aiki.
SHAWARA GA ABOKANAN SANA’ARSA
Shawarar da zan bawa ire-iren abokan sana’ata shi ne, na farko dai su sani, aikinmu aiki ne mai dauke da hatsarin gaske, domin aiki ne na sirri. Saboda akwai makarantu masu yawa suna kawo mana aikin buga takardun jarabawa, wanda ba a son kowa ya san kai a ka bawai aikin. Sannan aiki ne wanda yake son gaskiya da rikon amana. Sannan sana’a ce wadda idan mutum ya rike ta da zuciya daya zai ci ribarta har ya taimaki wasu. Wannan iya abin da zan iya cewa kenan a takaice.
TAMBIHI
Abubakar Zango kwararren matashi ne ta fuskar sanaar buga takardu, waatau (printing). Ya yi suna matuka a wannan sana’a ta buga takardu, shi ya sa wannan karon mu za su tura.
An haifi Abubakar Abubakar Zango a Garin Zango Kataf da ke cikin Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Mayu, 1980. Ya yi karatunsa na firamare a Kaduna Capital School, sannan ya wuce Kwalejin tunawa da Sardauna, wato Sardauna Memorial College Kaduna. Daga bisani ya wuce kwalejin kimiya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke kaduna, wato Kaduna Polytechnic.
Zainab matashiya ce yar kimanin shekara 18 da haihuwa, ba fara ba ce sosai (chocolate color) ce, tana da manyan idanuwa, bakinta daidai misali, hancin ta ma daidai misali. Faffadar fuska gareta, me matsakaicin tsayi ba tada kiba sosai amma kuma ba za a kirata da siririya ba, tana da kyan diri. Zainab dai ba laifi tana da kyanta, don ta hada dukkanin abubuwan da ake bukatar ganin ‘ya mace da shi.
Bangaren ilmi ma ba a bar ta baya ba, domin Zainab tana da Ilmin addini da na zamani. Ba ta wasa wajen zuwa Islamiyya, inda kusan duk shekara ita ke kan gaba a jarabawa. Har ila yau a makarantar boko, tuni ta kammala Sakandire a Kano Royal Academy.
Mahaifinta Alhaj Tukur Abdullahi attajiri ne, wanda ya shahara sosai kasancewar Allah ya yi masa arziki. Ya rasu tun Zainab na karama ita da kanwarta Habiba. Ya bar mahaifiyarsu Hajiya Sakina tare da yayansu; Mustapha, wanda suke kira da Yaya Musty.
Mahaifinsu dan asalin Jihar Kaduna ne, mahaifiyarsu kuma ‘yar asalin garin Birnin Kudu ce, yanayin kasuwancinsa ne ya sa shi zama a garin Kano har yayi aure ya haifi ‘ya’ya, kafin Allah ya dauki ransa.
Asalin sunan ta Zainab Tukur Abdullahi amma yanayin makaranata sai ake kiranta da Zainab Abdullahi Tukur, daga karshe ma aka koma kiranta da Zainab Abdullahi ba tare da an ce tukur din ba, kawayenta kuwa suna kiranta da Zainab Zeey Colour saboda iya kwalliyarta cikin kayan makaranta.
Zainab na da aminiya da ake kira Khadija, amma an fi yi mata lakabi da Precious. Tare suka kammala makaranta sun shaku da juna sosai.
Ranar wata Asabar da rana suka hadu a bikin Imaan Habib, kawarsu ce wadda ita ma suka gama makaranta tare. A duk lokacin da suka hadu Precious takan bawa Zainab labarin saurayin da ta hadu da shi. Yanzun ma labarin Saif din ne ta cigaba da yi mata shi, tana yaba haduwarsa. Takan ce “Saif yana da kyau sosai, ga shi ya iya kwalliya, rayuwarsa tana burge ni”.
Babban abinda ya fi daukar hankalin Precious kan Saif bai wuce iya kwalliyarsa da kuma kyan da Allah ya yi masa ba, wannan ya sa take kasa jure fadansa a koyaushe.
Cikin mamaki Zeey Colour ta kalli Precious a hankali kuma ta saki wani irin murmushi tare da cewa, “Ke dai har yau labarinki ba ya wuce na Saif.” Murmushi Precious ta yi me kwantar da zuciya ta ce, “Hmm.! Ai don ba ki gan shi bane, kin ji wani suna ma da suke fada masa?”
Ita dai Zainab ta zuba mata ido tana kallon ta kawai a hankali, sannan ta ce, “sai kin fada” Precious ta dada gyara zama ta ce “Usy Mam suke ce masa, kin ga yanzu ma har na karbi wata lambar.”
Zainab dai abun mamaki yake ba ta sai dai kuma ba ta nuna mata bakin cikin hakan ba sai na kuskuren da ta yi.
Zan ci gaba