• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Gabon 

by Sadiq
2 years ago
Gabon

Gabon, Kasa ce da ke Yammacin gabar tekun Afirka ta Tsakiya, sannan kasa ce da Allah ya albarkace ta da yalwar dazuka da kuma namun daji iri daban-daban, sannan suna da sadaukar da kai don ci gabansu.

Kazalika, Gabon kasa ce da ta ke da burin dorewa a matsayin kasa don samun ci gaba mai dorewa, da nufin kare albarkatun kasa tare da bunkasa tattalin arzikinta.

  • Sojojin Gabon Sun Kama Dan Hambararren Shugaban Kasa Da Laifin Cin Amanar kasa.
  • Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Gabon

Har zuwa safiyar ranar Laraba, Gabon ta kasance karkashin mulkin Shugaba Bongo tun shekarar 1967.

Hambararren shugaba Ali Bongo Ondimba ya kasance dan marigayi Omar Bongo, wanda shi ne shugaban kasar Gabon na biyu daga shekarar 1967 har zuwa mutuwarsa a shekarar 2009.

Bayan mutuwar mahaifinsa, Ali Bongo ya lashe zaben shugaban kasar Gabon na 2009, inda ya zama shugaban kasar na uku.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

An sake zabensa a shekarar 2016, a zabukan da aka yi mai cike da cece-kuce na rashin bin ka’ida, take hakkin dan Adam, da zanga-zangar bayan zabe da tashin hankali.

An kuma ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 na Gabon mai cike da cece-kuce. A ranar 30 ga watan Agusta, 2023 ne dakarun sojin Gabon suka yi juyin mulki na biyu a tarihin Gabon tun bayan samun ‘yancin kan kasar a shekarar 1960, inda suka yi juyin mulki na farko a shekarar 1964.

Abubuwa 10 na musamman game da Gabon:

1. Yalwar Dazuka: Gabon tana alfahari da yawan dazuka a kasar, wanda hakan ke taimaka mata wajen bunkasa tattalin arzikinta.

2. Mayar Da Hankali Kan Ci Gaba: Ƙasar ta himmatu wajen samar da ci gaba mai dorewa, ta hanyar kebe wani yanki mai yawa na kasart matsayin wuraren shakatawa kamar irin su Loango National Park, wanda ke ba da kariya ga namun daji da sauran wuraren shakatawa da ke bakin teku.

3. Bambance-bambancen Al’adu: Gabon kasa ce mai kabilu sama da 40, kowannensu yana da al’adunsa da harsuna daban-daban.

4. Manyan Namun Daji: Kasa mai tarin manyan namun daji kamar irin su giwaye, gwaggon biri, macizai da sauransu.

5. Wuraren Shakatawa: Wannan ya kunshi muhimman wuraren shakatawa da masu yawon bude ido ke zuwa wanda yawanci dabobbi ke nishadantar da masu ziyara.

6. Kare Muhalli: Gabon ta yi kaurin suna wajen kare muhalli ta hanyar bai wa tsirrai da hallitu kulawa ta musamman.

7. Yawon Bude Ido: Kasar tana ba da dama don yawon shakatawa da bude ido, wanda baki ke ziyarta don ganin nau’ikan halittu na musamman.

8. Karacin Mutane: Duba da rashin yawan al’ummar kasar, Gabon tana kiyaye daidaito tsakanin ayyukan dan adam da yanayin kasar.

9. Masana’antar Mai: Duk da kasancewarta kasa mai fitar da mai, Gabon ta dauki matakai don rage tasirin muhalli da saka hannun jari kan tsirrai.

10. Kasa Mai Cike Da Al’adun Gargajiya: Kasar na da tarin al’adun gargajiya sannan ta samu ci gaban zamani ta hanyar samun abubuwan more rayuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kano
Manyan Labarai

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Next Post
Wang yi

Ministan Wajen Sin Ya Tayawa Takwaransa Na Najeriya Murnar Kama Aiki Ta Wayar Tarho

LABARAI MASU NASABA

Kano

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.