Jam’iyyar APC mai mulki ta dage taronta na kwamitin koli na kasa da na kwamitin zartarwa na kasa har zuwa wani lokaci.
Jam’iyyar APC ta tsayar da ranakun 11 da 12 ga watan Satumba domin gudanar da tarukan kwamitoci guda biyu, biyo bayan amincewar da Shugaba kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Aiki Tare Da Kasashen Duniya Wajen Sa Kaimi Ga Raya Sha’anin Mutane Masu Bukata Ta Musamman
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 49 A Yankuna 226 A Kano — SEMA
Jam’iyyar ta kuma umurci mambobin kwamitocin guda biyu da su halarci taron.
Sai dai sakataren yada labaran jam’iyyar APC na asa, Barista Felid Morka ya sanar da dage taron biyu a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, “Ana sanar da mambobin kwamitin koli da na kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar APC cewa, tarukan da aka shirya gudanarwa a ranakun 11 da 12 ga Satumba, 2024, an dage su har zuwa wani lokaci.”
Jam’iyyar ba ta bayyana dalilan da ya sa ta dage tarukan ba, amma ana ganin cewa jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne saboda shugaban kasa baya nan.
Babban sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta gudanar da babban tarukan ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sakataren ya ce tarukan za su duba halin da jam’iyyar ke ciki da samar da hanyoyin magance kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta da zayyana wasu dabaru da za a aiwatarwa domin samun nasarar jam’iyyar.
Kwamitin koli na kasa na jam’iyyar APC ya kunshi dattawa da wasu daga cikin manyan jami’ai da shugabannin majalisa da masu mataimaka wa jam’iyyar wajen cimma matsaya kan batutuwan da za a tattauna a taron kwamitin zartarwa.
Haka kuma kwamitin na bayar da shawara ga jam’iyya da shugaban kasa.
Ana sa ran Shugaban Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima za su halarci tarukan.
Sauran wadanda ake sa ran za su halarci tarukan sun hada da manyan mambobin kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar APC (NWC), karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje, tsohon shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa wadanda ’yan jam’iyya ne, manyan jami’ai na majalisar dokokin kasa na da da na yanzu, da tsaffin shugabannin jam’iyyar na kasa da sakatarorin jam’iyyar da jiga-jigan jam’iyyar guda biyu kowanne daga sassar kasar nan.
Basiru ya ce taron zai yi la’akari da rahoton binciken kudi na shekarar 2023/2024 tare da amincewa da kasafin kudin jam’iyyar na shekara mai zuwa.
Ya ce wani muhimmin abu a cikin ajandar taron shi ne, sake duba rajistar jam’iyyar APC, wanda ake sa ran zai kara kaimi ga mambobin jam’iyyar da kuma samar da sahihin bayanai game da adadin mambobin jam’iyyar a fadin kasar.
Ya kara da cewa, gabanin tarukan, jam’iyyar ta kaddamar da cibiyar ci gabanta a wani bangare na kokarin da take yi na gyara akidarta da kuma bayar da horo ga ‘ya’yan jam’iyyarta.
Basiru ya ce, “Taron zai kayyade ranar da za a gudanar da babban taron da ba na zabe ba. Babban taron kasa shi ne mafi girman tsarin yanke shawara na jam’iyyar. Muna da nau’i biyu na al’ada. Na farko shi ne, taron zabe. Bayan haka, muna kuma da babban taron tsakiyar wa’adi, wanda ba zababbu ba ne. Shugabannin jam’iyyar ne za su yanke hukunci kan haka.
“Tarukan za su sake duba zabukan da suka gabata da kuma da tsara yadda za a gudanar da zabukan Edo da Ondo, wanda za a yi a wannan watan da Nuwamba.”
Basiru ya ce bai san da rade-radin da ake yi cewa taron kwamitin zartarwa zai tantance makomar wasu jami’an jam’iyyar ba.
“Duk wani abu da ba a cikin ajandar tarukan ba mu sanan shi ba.”