- Yadda Abin Ya Faru –Ganau
- Tabbas ‘Yan Ta’adda Muka Farmaka –NAF
Al’ummar Kauyen Jika da Kolo da ke garin Yadin Kidandan a karamar hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna na ci gaba da zaman dar-dar bisa zargin kai musu hari da jiragen sojin saman Nijeriya ya kai musu a makon da ya gabata.
Al’ummar garin sun zargi sojojin sama da jefa musu bam yayin da suke gudanar da sallar Juma’a a cikin masallaci da kuma kasuwa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 23.
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Za Su Kaɗa Ƙuri’ar Kawo Canji Na Gaskiya A 2027 – Kwankwaso
- Gwamna Sani Zai Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Cutar Kansa Mai Gadaje 300 A Kaduna – Kwamishina
Harin bam din ya haifar da cece-kuce tsakanin al’ummar garin da runduna sojin saman Nijeriya, inda mutanan kauyen suke zargin sojoji sun kai harin mai uwa da wabi.
Sai dai a nata, bangaren rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta wanna zargi, ta kuma bayyana cewa harin da ta kai ya tafi kai tsaye ne ga sansanin babban dan bindiga mai suna Kadade Gurgu, wanda na hannun daman dan ta’adda Dogo Gide ne.
A wata ziyara da wakilinmu ya kai a yankin karamar hukumar Giwa, wasu mazauna garin sun bayyana cewa akwai fararen hula da harin sojojin ya shafa.
Haka zalika, sun kamanta harin da sojojin suka kai da wanda aka kai a baya a garin Tudun Biri, wanda ya yi sanadiyyar rasa ran masu Mauludi kimamnin guda 100 a watan Disamban 2023.
Wani magidancin dan asalin garin Kidandan, ya bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru, yana mai cewa, “Bisa batun tsaro ba zan iya bayyana sunana ba, amma dai ni dan asalin garin Kidandan ne kuma a nan aka haife, sannan a nan nake rayuwa, bisa matsalar tsaro ya sanya muke zuwa garin jifa-jifa.
“Yadin Kidandan gari ne wanda ya zama sansanin ‘yan ta’adda. Wanda yanzu shiga garin idan kai ba dan gari ba ne ba ya shiguwa. Ranar Juma’ar da ta gabata, wani jirgi ya kai hari har ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Amma batun gaskiya shi ne, har yanzu babu wani wanda zai iya tantance cewa wadanda suka mutu a harin ‘yan garin ne kadai babu ‘yan ta’adda a ciki, saboda gari ne wanda yake cakude da mutanan kirki da ‘yan ta’adda.”
Wani mazaunin garin Jika da Kolo da ke zaune a garin Gwargwaji a Zariya ya shaida cewa, “Yawancinmu har yanzu muna zaune a kusa da kauyen, saboda ba mu da wani wurin da za mu koma. A nan aka haifi kakanninmu.
Mun rasa ‘yan uwanmu da yawa, ciki har da yara marasa laifi.
“Kuma batun cewa harin ya rusa da masallaci ba haka ba ba ne. An dai kashe mutane amma harin bai taba masallaci ba.”
Sai dai wani bincike da LEADERSHIP HAUSA ta gudanar ya nuna cewa masallacin da al’ummar garin na Jika da Kolo suke zargin sajojin sun kai hari, dan siyasa daga Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Amin “Little”, ya gina musu. Wanda yake kusa da wat babbar gonarsa da ke yankin domin gudanar da sallar Juma’a.
Majiyarmu ta shaida mana cewa shekaru biyu baya, shi kansa dan siyasar ya tsallake rijiya da baya daga hannun ‘yan ta’adda, inda aka harbe shi a hannu, lamarin da sanya ya dakatar da zuwa gonar bisa matsalar rashin tsaro.
A wata sanarwar da rundunar sojan sama ta fitar ta hannun daraktan yada labaranta, Kaftin Kabiru Ali, ya jaddada cewa ba su Kai hari a masallaci ba, kuma duk wani bayani zai zo ne bayan da rundunar ta kammala bincike.
Rundunar ta kara da cewa ta kashe ‘yan ta’adda da dama yayin harin da ta kai, amma babu masallaci a wurin da jiragen suka kai harin.
A wata zantawa da ya yi da wakilinmu, Kansilar Mazabar Kidandan, Abdullahi Ismail, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kauyen Jika da Kolo ya zama sansanin ‘yan ta’adda da suke cin kasuwarsu babu babbaka.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa an yi jana’izar mutane da suka ransu su 23.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kwamshinan harkokin tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan kan lamarin, inda ya kira wayarsa har sau uku bai dauka ba.