Hasasahe na nuna da cewa, akwai yiwuwar abinci ya kara tsada a bana. Dalilai da yawa suka sa ake wannan hasasahen.
Dalili na farko da masanan suka bayyana shi ne, ambaliyar ruwa a wadansu jihohin Nijeriya, wanda hakan zai sa, a yi asarar amfani mai yawa a wasu jihohin da ke kasar nan.
Yanzu haka maganar nan da ake yi wannan hasashe na masama ya tabbata a wasu jihohin Arewacin Nijeriya, irin su, Sakkwato da Nasawa da kuma wasu jihohin Arewacin Nijeriya.
Wani abu da masanan suka bayyana a matsayin abin fargaba, na abin da zai sa abinci ya yi tashin gwauron zabo shi ne, fargabar da manoman ke yi na rashin tsaro, wamda ya sa musamman manyan manoma sun kaurace wa noman a bana, wanda hakan ta rage yawan noman da ake yi, hakan kuma na nuna cewa, akwai yiwuwar abinci ya yi tsada a bana.
Baya ga tsadar takin zamanin, manyan manoma sun koka da tsarar man da za a zuba wa inji domin ban-euwa lokacin noman rayi da kuma tsadar iri.
Wani babban kalubalrn kuma shi, tsadar aikin, musamman da yake wadanda ake dauka aikin a halin yanzu na fargabar shiga gonakin domin yin aikin sabida barazanar tsaro.
Wani manomi mai suana Alhaji Umaru Dikko da zaune a karamar hukumar Giwa ya tabbatar da cewa, yanzu haka dole ta say a kasa zuwa wasu gonaki nasa da yake nomawa.
Haka wani manomi mai suna Husaini da ke garin kaya, a karamar hukumar ta Giwa, shi ma ya ce, dole ta sa sun bar gonakin nasu, musamman ganin yadda ‘yan bindigar har yanzu ba su daina kai hare-hare ba, wanda a kwanan nan suka kwashi mutane a garin Yakawada.
Baya ga jihar Kaduna, irin wannan barazana ta ‘yan bindiga ta tauye ci gaban noma a Zamfara, yayin da ‘yan bindigar ke kama manoman suna kashe wa, wani lokacin kuma su karbi kudin fansa.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa, ‘yanbindigar na cin karensu ba abbaka a wasu sassan karamar hukumar Giwa.
Wadannan abubuwa na daga cikin abubuwan da ake hasashen cewa, za su sa abinci ya yi tsada a bana.
Wani abu da ya rage yawan noman da ake a bana shi ne, yadda wasu gwamnatocin jihohi suka tsame hannunsu dangane da tallafin da suke bai wa manoman.
Haka kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa, akwai wata cuta da ta bulla musamman a wasu sassa na jihar wassa ke kama masara da dawa, wanda wasu manoman da yawa su bayyana wannan cutar a matsayin babbar barzana ga amfanin gonar na bana.
Wadannan abubuwa da aka ambata na daga cikin abubuwan da suka sa, ake hasashen cewa, akwai yiwuwar abinci a bana ya kara tsada.