Majalisar dattawa ta bayyana damuwarta kan matsalar tsaro da ake fama da shi a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ta ce a yanzu haka birnin na fuskantar barazana da kuma rashin kwanciyar hankali.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa babban abun takaici ne a kusa cikin Abuja har akai farmaki a wurare kamar irinsu Kubwa, Bwari da dai sauransu.
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da ‘Yan Wasan Super Eagles -Tinubu
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari -Fintiri
Akpabio ya yi Magana ne kafin majalisa ta dage zaman zuwa mako mai zuwa da shugabannin tsaro sakamakon rashin halartar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da shugaban tsaro na kasa, Christopher Musa.
A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ta caccaki shugabannin tsaro saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta a Nijeriya tare da jan kullensu na kawo karshen matsalar.
Majalisar da dai gayyace su ne sakamakon kasha-kashen da garkuwa da mutane da ake samu a wasu yankunan kasar nan ciki har da Abuja.
Sai dai kuma an dage zaman ganawar har zuwa ranar 13 ga Fabrairu bayan da mazalisar dattawan ta amince da rashin da uzurin da wasu wadanda ya kamata su halarci taron amma ba su sami zuwa ba Akpabio ya ce an dage ganawa da shugabannin tsaron ne saboda wadanda aka zayyata ba duka ba ne suka zo. Ya ce akwai bukatar babban hafsan tsaro da shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ahmed Rufai da ministan harkokin ‘yansanda su halarci wannan ganawar domin a yi nazari a kan lamarin
Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban majalisar dattawa ya ce, “Lamarin ya kazanta a Agatu da ke Jihar Taraba, Oyo, Filato a yankunan Mangu, Bokkos, Barkin Ladi. Haka kuma muna bukatar cikakken bayani kan yadda ‘yan bindiga suka kwararo har Abuja, yankuna irin su Kubwa da Bwari,” in ji Akpabio.