Abba Ibrahim Wada" />

AC Millan Za Ta Kori Gattuso Ta Daiki Conte

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta AC Millan ta fara shirye shiryen korar mai koyar da ‘yan wasan kungiyar wato Gannaro Gattuso domin daukar Antonio Conte.
Conte yabar Chelsea bayan da kungiyar ta koreshi inda ta maye gurbinsa da Mauricio Sarri, dan kasar Italiya duk da cewa Conte ya lashe kofin Firimiya da kuma gasar cin kofin kalubake ta FA cikin shekaru biyu a kungiyar.
A kwanakin baya an ruwaito cewa Conte yana shirin kai kungiyar Chelsea Kotu, bayan dayayi zargin cewa kungiyar ta cuceshi saboda bata koreshi da wuri ba gashi har lokaci ya kure wajen neman sabuwar kungiya.
Gattuso dai yakai AC Millan matsayi na shida a kakar wasan data gabata kuma ya buga gasar cin kofin Europa da kungiyar ta AC Millan sai dai kasancewa Conte Bashi da kungiya zaisa kungiyar ta koreshi.
Conte dai yanada kwarewa a gasar siriya bayan ya lashe kofin siriya A guda uku da kuma kofin kalubale guda uku da kungiyar Jubentus acikin shekaru uku da yayi da kungiyar kafin kuma ya koma ya karbi tawagar kasar Italiya.

Exit mobile version