ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Adadin Kuskuren Da VAR Take Tafkawa Ya Ragu A Wannan Kakar

by Abba Ibrahim Wada
9 months ago
Var

Shugabannin da ke lura da gasar kwallon kafa ta Premier a Ingila sun bayyana cewa na’urar da ke taimaka wa alkalin.

wasa wajen yanke hukunci (VAR) ta tafka kuskure sau 13, tun bayan fara wannan kakar ta sheakarar 2024 zuwa 2025 da ake bugawa a daidai wannan lokaci, matakin da masu sharhi a kan kwallon kafa suke ganin akwai bukatar a tashi tsaye domin kauce wa wasu kura-kuren

  • Shekara Ɗaya A Ofis: An Buɗe Gasar Cin Kofin Babban Hafsan Sojojin Nijeriya A Katsina
  • Babbar Gasar Wasannin Kankara Ta Zama Damar Tabbatarwa Duniya Niyyar Karfafa Zaman Lafiya

Hakan na nufin an samu raguwar kurakuran da na’urar ke yi idan aka kwatanta da kakar da ta gabata, inda ya zuwa irin wannan lokaci ta tafka kuskure sau 20.

ADVERTISEMENT

Na’urar ta yi kuskuren sauya hukuncin alkalin wasa sau hudu sannan ta yi kuskuren rashin sauya hukunci sau tara a cikin wasanni 23 da aka buga, kamar yadda kwamitin alkalan da ke lura da takaddamar da ake samu a lokacin wasa.

An samu lokuta 70 da aka yi amfani da na’urar ta VAR a wasanni 279 na gasar Premier a wannan kakar ya zuwa yanzu, kwatankwacin amfani da na’urar sau daya a cikin wasa uku.

LABARAI MASU NASABA

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata.

“Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes.

Ya ci gaba da cewa “Mun san cewa kuskure daya tal zai iya cutar da kungiya. Sakamako da kuma makin da kungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horarwa ko kuma dan wasa ya rasa damarsa a cikin kungiya.”Hakan ya faru ga Erin ten Hag – domin daya daga cikin kurakurai hudu da na’urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a wasa na karshe da kocin ya jagoranci kungiyar Manchester United.

Haka nan wasu alkalan wasan sun fuskanci cin zarafi, inda a kwanakin nan ‘yansanda suka kaddamar da bincike kan “barazanar cin zarafi” kan alkalin wasa Michael Oliber bayan wasan da Arsenal ta yi nasara kan Wolbes da ci 1-0 a watan Janairu. Kuma wannan ya biyo bayan matakin da alkalin wasan ya dauka na bai wa dan wasan Arsenal, Myles Lewsi-Skelly katin kora – matakin da daga baya aka soke bayan korafin da kungiyar ta shigar.

Shi ma tsohon alkalin wasa Dabid Conte, an kore shi ne a watan Disamba bayan binciken da aka gudanar a kansa. Hukumomin gasar Premier dai ba su bayyana lokuta 9 da na’urar VAR ta ki soke wani mataki ba – kuma babu tabbas ko batun jan katin da aka bai wa Lewis-Skelly na ciki amma hukumar ta yi bayani kan kurakurai hudu da na’urar ta tafka ga manema labarai.

Kuskure hudu da VAR ta tafka

Outtara ya ‘taba kwallo da hannu’ – Bournemouth 1-1 Newcastle, 25 ga Agusta.

Abin da ya faru: Dango Outtara ya zaci cewa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallon da za ta ba ta nasara lokacin da ya zura kwallon da kai. Lafari Dabid Coote ya bayar da kwallon.

Matakin VAR: Mai kula da na’urar VAR a wasan, Tim Robinson ya bai wa Coote shawarar soke kwallon, inda ya ce an taba kwallon da hannu. Kasancewar yana da yakini kan hukuncinsa, bai bukaci lafari ya kalli bidiyon lamarin ba.

Sakamako: Kasancewar babu cikakkiyar hujjar da za ta tabbatar da cewa kwallon tabbas ta taba hannun Ouattara, shugaban hukumar lura da alkalan wasan gasar Premier, Howard Webb a lokacin da ya tattauna da kafar yada labarai ta Sky Sports, ya ce – VAR ta yi kuskure wajen soke cin kwallon.

 

De Ligt ya kwashe Ings – West Ham 2-1 Man Utd, 27 ga Oktoba

Abin da ya faru: Xan wasan gaba na West Ham, Danny Ings ya fadi a cikin yadi na 18 lokacin da yake fafutikar buga kwallo tsakaninsa da mai tsaron baya na Manchester United, Mathijs de Ligt. Lafari Dabid Coote ya bayar da damar a ci gaba da wasa amma sai mai kula da na’urar VAR, Michael Oliber ya bukaci a sake dubawa a talabijin na gefen fagen wasa.

Matakin VAR: Daga nan ne Coote ya bayar da bugun fanareti, wanda dan wasa Jarrod Bowen ya zura a raga, kuma hakan ya bai wa West Ham nasara a wasan.

Sakamako: Washegari United ta sallami Ten Hag daga aiki. Daga baya Web ya ce bai kamata a bayar da fanaretin ba.

 

Jan katin da aka bai wa Norgaard – Brentford 0-0 Eberton, 23 ga Nuwamba

Abin da ya faru: Xan wasan Brentford, Christian Norgaard ya tokari mai tsaron ragar Eberton, Jordan Pickford a gwiwa lokacin da suke fafutikar kaiwa ga kwallo a cikin yadi na 18.

Mataki VAR: Alkalin wasa Chris Kabanagh bai ce an yi keta ba amma sai mai kula da na’urar VAR ya bukace shi ya sake duba wurin a talabijin din gefen fage. Bayan sake dubawa, nan take ya daga wa Norgaard jan kati.

Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa ya soke dakatarwar da aka yi wa Norgard na wasa uku bayan korafi da kungiyar ta Brentford ta shigar.

Soke kwallon da Milenkobic ya zura – Nottingham Forest 3-2 Southampton, 19 ga Janairu.

Abin da ya faru: Nikola Milenkobic ya jefa kwallo a raga da kai inda hakan ya sanya Nottingham Forest ta yi gaba da ci 4-1.

Matakin VAR: Na’urar VAR ta umarci lafari Anthony Taylor ya soke cin saboda dan wasan Forest, Chris Wood ya yi satar fage inda hakan ya hana masu tsaron baya na

Southampton damar kalubalantar kwallon. Wood bai taba kwallon ba.

Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa da ya duba lamarin ya ce ya kamata a bayar da cin.

Shin Ko Barcelona Ce Matsalar Dembele?

Tauraruwar dan wasa Ousmane Dembele tana ci gaba da haskawa tun bayan barinsa kungiuar kwallon kafa ta Barcelona inda ya ci gaba da saka kwazo a cin kwallaye, bayan da Paris St-Germain ta je har gida ta doke Brest 3-0 a wasan cike gurbi a Champions League ranar Talata inda Dembele ya zura kwallo biyu a raga karo na 10 yana cin kwallaye a jere a PSG, kuma na 18 jimilla a wasa 11 baya a dukkan fafatawa.

Xan wasan tawagar Faransa ya ci uku rigis a gasar zakarun Turai da Stuttgart kuma a tarihi wasu ‘‘yan wasa kadan ne da suka zura kwallo uku rigis a wasa biyu a jere a Champions League da ya hada da Lionel Messi a Barcelona a 2016 da Cristiano Ronaldo a Real Madrid a 2017.

Dembele bai samu kafa wannan tarihin ba, wanda aka sauya shi da Goncalo Ramos a minti na 82 a fafatawar. Kenan Dembele ya ci kwallo 14 a Ligue 1 da Champions League a 2025.

Tun kafin Dembele ya zura biyu a ragar Brest, Vitinha ne ya fara ci a bugun fenariti a minti na 21 da fara wasan kuma wannan shi ne wasan farko zagayen cike gurbi a sabon fasalin Champions League, za su kara a wasa na biyu a Paris ranar 19 ga watan Fabrairu. PSG, wadda ba ta taba daukar Champions League ba, an kusan fitar da ita a gasar bana a cikin rukuni, daga baya ta kara kwazo da ta doke Manchester City da Stuttgart a wasanninta na gaba.

Ana sa ran PSG za ta kai zagayen gaba cikin ruwan sanyi, wadda ake sa ran watakila ta fuskanci Liberpool ko kuma Barcelona a zagayen ‘yan 16.

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika
Wasanni

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

November 17, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
Nazari

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
Wasanni

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Next Post
Yadda Mata ‘Yan Ƙasar Nijar Suke Tururuwar Neman Lafiya A Nijeriya

Yadda Mata 'Yan Ƙasar Nijar Suke Tururuwar Neman Lafiya A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

November 17, 2025

MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi

November 17, 2025
Tinubu

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

November 17, 2025
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

November 17, 2025
Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika

November 17, 2025
Tsohuwar Firaministan Bangaladesh Sheikha Hasina,

An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.