Jam’iyyar Hadaka ta ADC ta soki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da wutar lantarki ke ciki a kasar nan, tana mai cewa ya yi alkawarin samar da wutar lantarki mai dorewa ga ‘yan Nijeriya cikin shekaru hudu a tsawon 24, amma har yau wutan lantarkin ba ta samu ba.
Sakataren yada labarai na wucin gadi na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya tunatar da shugaban kasa game da alkawarinsa na bayar da wutar lantarki ba tare da tangarda ba, yana mai jaddada tsohon bidiyon kamfen inda Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da wutar lantarki na tsawon awo 24 ga wanaki 7.
- Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
- Tinubu Na Yi Wa Arewa Manyan Ayyuka – Martanin Fadar Shugaban Ƙasa Ga Kwankwaso
Abdullahi ya ce, “A yau muna tunatar wa ‘yan Nijeriya cewa Shugaba Tinubu ya yi alkawarin samar wa ‘yan Nijeriya tsayayyen wutar lantarki ba tare da tsangwama ba cikin shekaru hudu. Amma har yanzu ba mu gani a kasa ba.”
Abdullahi ya ci gaba da zayyano kurakuran da gwamnatin ta yi a fannin wutar lantarki, yana mai cewa tun bayan da Tinubu ya karbi mulki, an kara kudaden wutar lantarki da kashi 240, yayin da babban tashar wutar lantarki ta kasa ta fadi har sau 12.
“Fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 90 na fama da rashin wutar lantarki a halin yanzu, yayin da yawa ke samun wutar lantarki na awanni 4 zuwa 6 a kowace rana a karkashin tsarin Band A-E na Tinubu da ya gaza. A cikin kauyuka kuwa, mafi yawancin iyalan miliyan 50 na Nijeriya suna nan cikin duhu sakamakon katsewar babban layin wutar lantarki, wanda ya janyo rashin samun wutar lantarki na tsawon watanni,” in ji shi.
Ya zargi gwamnatin da cewa ba ta dauki kwararan matakai na kawo babban gyara a fannin wutar lantarki ba, sannan ta gaza wajen nuna wani hobbasa game da lamarin ballantana har kuma ta dauki matakin gaggawa a cikin shekaru biyu da ta kwashe tana mulki.
“Mun wuce rabin lokacin wannan gwamnatin, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya na ci gaba da caji wayoyinsu a tashoshin caji na hannu, suna kashe dubban naira wajen sayen man fetur na janareta domin samun wutar lantarki.
“Ina hasken wutan lantarkin da aka yi wa ‘yan Nijeriya al’kawari? Me ya faru da alkawarinku? Kuma har yaushe ‘yan Nijeriya za su ci gaba da zama cikin duhu?”
Ya sake dawo wa da alkawarin Tinubu a lokacin yakin neman zabe, ya ce, “Mai Girma Shugaban Kasa, ka taba cewa, ‘Idan ban gyara wutar lantarki ba, ka da ku sake zabe na.’ Kuma ‘yan Nijeriya sun ji wannan. Za mu cika maka burinka a 2027.”
Bidiyon kamfen da Abdullahi yake yadawa a kafafen sadarwa na zamani, ya nuna inda Tinubu yake, “Zan bi duk wata hanyar na samur da cikakken wutar lantarki. Kuma ba za ku sake biyan kudin wutan lantarkin da ba ku shafa. Kyan alkawari cika. Idan ban cika alkawarin da na yi muku ba, ko na dawo neman a zabe ni a karo na biyu, kar ku zabe ni.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp