Tsohon ɗan majalisar Dattijai mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) za ta samar da ɗan takara mai ƙarfi da zai kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Melaye ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a shirin Politics Today ranar Juma’a, inda ya ce dole ne a daidaita jam’iyyar kafin a fitar da dan takarar shugaban kasa. Ya ce, “Ina da yakini cewa ADC za ta samar da dan takara da zai kayar da Tinubu a 2027.”
Sanatan da ya koma ADC kwanan nan tare da wasu fitattun ‘yan adawa, ya ce yanzu burinsa ba na mutum ɗaya ba ne, sai dai gina jam’iyya mai haɗin kai da inganci. Ya ƙara da cewa, “Ba zan faɗi wani ɗan takara ba har sai mun yi taron jam’iyya cikin gaskiya da adalci, sannan mu fitar da ɗan takara nagari.”
- Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
- 2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa
Melaye ya kwatanta ADC da wani sabon tunani na “kiran tuba,” yana mai cewa wannan jam’iyya ce da ‘yan Nijeriya ke komawa don neman gaskiya da shugabanci mai imani. Ya ce, “ADC wani mambari ne na ƙasa don masu kishin Nijeriya da ke neman sauyi.”
Taron haɗin kan ‘yan adawa da aka gudanar a ranar 2 ga Yuli a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua a Abuja, ya tabbatar da wannan yunƙuri. A taron, an bayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riƙo na haɗin gwuiwar, yayin da Rauf Aregbesola ya zama sakatare. Fitattun ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, da Peter Obi, da Nasir El-Rufai, da Rotimi Amaechi, da Dele Momodu da Emeka Ihedioha sun halarci taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp