Musa Ishak Muhammad" />

Addu’o’i Da Shawarwarin Iyaye Su ne Silar Nasarata – Mawaki Nasir Kanawy

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da MAWAKI NASIR MUSA ALIYU Wadda A Ka Fi Sani Da Nasir Kanawy.

Da Farko Dai Za Mu So Ka Fada Mana Cikakken Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.

Assalamu alaikum warahmatullah, ni dai sunana Nasir Musa Aliyu, wanda a ka fi sani da Nasir Kanawy. An haife ni cikin garin Kano, Kwanar Diso, a Karamar Hukumar Gwale. Amma daga baya mun taso mun dawo Shagari Kuarters. A nan Shagari Kuarters na girma na tashi na yi wayo. Na yi karatuna na Firamare a makarantar Badar Nursery and primary school Dan Agundi. Sannan na yi sabuwar Kofa, sannan na yi Kano Day Science. Na gama Diploma dita a School of Technology, sannan na yi karatun Degree a Open Unibersity, inda duka na karanta Computer Science.

Ya Ya A Ka Yi Ka Sami Kanka A Cikin Harkar Waka?

To ni dai na samu kaina a harkar waka ne, kasan mu daman chan a al’adar Hausa mu na da wakoki namu irin na gargajiya, wanda iyayenmu su ke yi tun mu na kanana. To daga irin wannan wakokin ne ni idan ina ji sai in ringa jin su a zuciyata da salo kala-kala na Waka. To daman na dade da ra’ayin yin waka, wannan kusan shi ne yadda a ka yi na fara waka.

Yaushe Ne Ka Fara Waka?

Eh to gaskiya na dade da fara waka fa, domin na fara waka ne tun wajen 1999 zuwa 2000. Amma fan fara cewa zan rubuta waka ba sai wajen 2004. Kuma bayan wannan lokacin ne wakokin su ka fara futa. Da idan na yi kawai aiyewa nake, kuma na yi wakoki da yawa a lokacin. Kamar irin na yabo da na nanaye da sauransu. Wannan shi ne lokacin da na fara har kuma zuwa yanzu.

Wacce Iriyar Waka Ka Ke Yi?

Ni na fi yin wakokin Hip-hop, amma kuma ba irin wakar da ba na yi. Ina yin R and B, ina yin Hip-hop, ina wakokin nanaye da kuma wakoki na gargajiya.

Wacce Ce Wakarka Ta Farko Da Ka Fara Yi?

Wakar da na fara yi wata dadaddiyar waka ce gaskiya don tun a na samari. Waka ce mai taken “She is the only one for me”. Amma wannan an yi ta na tun ana samari sosai amma dai dadaddiyar waka ce gaskiya. Daga nan kuma an yi wakoki masu yawa, wasu an yi aikinsu wato an yi(recording), wasu kuma kawai dai an rubuta ne an ajiye.

Ya Ya Wannan Waka Ta Zo Maka Duba Da Cewa Ita Ce Wakarka Ta Farko?

Wakar ba ta zo min da wata wahala ba, kuma ina kallon ta a matsayin madafata, wadda na ke dafawa na gane dai-daina ko rashin dai-daina.

Wa Ne Kalubale Ka Fuskanta A Lokacin Da Ka Fara Waka?

Kasan a rayuwa ba zai yi wu a ce ba ka da kalubale, kadan daga ciki akwai kalubale na lokaci, kalubale na rashin kudade da kuma kalubalen kallon da wasu za su ringa yi maka a matsayin wanda ya lalace. Amma babban abun dai shi ne mu na neman Allah ya yi mana jagoranci.

Izuwa Yanzu Wakokinka Sun Kai Kamar Guda Nawa?

Ehh gaskiya wakokina ban san adadinsu ba izuwa yanzu. Kamar yadda na fada maka da kawai yi nake ina ajiyewa, amma yanzu needa na hadu da (Producer) mai kyau wato Dr. Nedcezz to shi ne ya fara saita ni, ya na ba ni shawarwarin yadda zan amfani baiwar da Allah ya bani. Saboda dai na yi wakoki da yawa amma ba zan iya fadar ga adadinsu ba gaskiya.

Ka Taba Fitar Da (Album) Ne Wato Kundin Wakokinka?

Eh yanzu ina aikin Album dina mai suna “Fuska Biyu” wanda ke shirin fitowa in sha Allah a watan uku na wannan shekarar, wato watan Maris (March).

A Cikin Tarun Wakokinka Wacce Waka Ka Fi So?

A cikin wakokina na fi son wata waka mai suna “tafiya”.

Me Ne Ne Yasa Ka Fi Son Wannan Waka Mai Suna Tafiya?

Gaskiya na fi son wakar tafiya ne, saboda na farko dai ka ga ta ba ni wahala sosai wajen rubutawa. Sannan abu na biyu, waka ce da take bayyana wayewa ta muamala da wadanda ba ka san su ba. Sannan wani abinda ya sa na ke son ita wannan waka shi ne, ita wakar rufi ce wato abinda a ke cewa(Cover) ta wani mawaki da na ke so sosai wato Michael Jackson.

To Wacce Waka Ce Kuma Ta Fi Wahalar Da Kai A Cikin Jerin Wakokinka?

Eh wakar da ta fi wahalar da ni ita ce dai wannan waka mai suna tafiya.

Ka Na Da Wani Maigida Ne Da Ya Ke Taimaka Maka A Cikin Wannan Harkar Ta Waka?

Gaskiya ni dai ba ni da wani maigida da ya ke taimaka mini. Taimako sai dai na iyaye, wanda daman su su ke saita mu, kuma su ke bamu shawarwari a kan yadda za mu tafi da lamuranmu. Sannan (producer) dina shi ma ya na taimaka mini da shawarwari, sai kuma ‘yan uwa da abokan arziki, da kuma ku ‘yan jarida da ku ke taimaka mana.

Ka Na Da Wani Mawaki Da Ka Ke Kwaikwayo Kuwa?

Eh ai duk mawaki ba zai rasa mawakin da ya ke haska masa gabansa. Ni ka ga a na gida ina sauraren Shata sosai kuma ina jin dadin wakokinsa. Sannan a kasashen waje ina irin su Michael Jackson, su 2Pac da sauransu.

Me Ne Ne Burin Da Ka Ke So Ka Cinma A Cikin Harkar Waka?

Eh burina shi ne wakokina su samu karbuwa da kuma yaduwa, sannan kuma sakonnin da su ke dauke da su, su Isa ga mutane. Wanda su ke na dai-dai su karba, wanda kuma ya ke ba na dai-dai ba su bar su, domin kowa ya na tare da dai-dai da kuma rashin dai-dai. Amma kodayaushe mu na kokari sosai wajen ganin mun kawo wakoki masu dauke sakonni masu muhimmanci ga mutane, ba sakonni na harigido ko yuya ba.

To Me Ne Ne Sakonka A Karshe Ga Masoyanka Masu Sauraren Wakokinka?

To sakona ga masoyana masu sauraren wakokina shi ne, ina sanar da su cewa ina kaunarsu kamar yadda su ke kaunata. Domin su masoya kai ne su, kuma su ne kai. Sannan ina kara kira gare su da su ringa nazartar wakokinmu su na daukar muhimman sakonnin ciki, Wanda kuma mu ka yi kuskure, tuntuben harshe ne sai a nuna mana domin mu gyara. Kuma ina kiran kaina da kuma su baki daya da mu guji wulakanta Dan Adam, domin Dan Adam ya na da girma sosai, kuma ba ka san wa zai taimake ka a rayuwa ba. Bissalam

Exit mobile version