Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya, Alhaji Ibrahim Gusau, ya ce bashi da wani shakku kan wasan da Super Eagles za ta kara da mai masaukin baki a gasar cin kofin Afrika da a ke yi yanzu haka a kasar Ivory Coast.
A hirar da ya yi manema labarai a Abuja, Gusau ya ce sun yi duk wani shirin da ya kamata domin tunkarar wannan wasa da za a yi yammacin ranar Alhamis.
- NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”
- Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
Dangane da wasan da Nijeriya ta buga a baya, Gusau ya ce suna bai wa magoya baya hakuri a kan abin da ya faru kuma a yanzu sun dauki mataki kuma hakan ba za ta sake faruwa ba.
Ya kara da cewa suna da kwarin guiwa sosai akan ‘yan wasan Nijeriya.
Kazalika, ya ce ba su da wata matsala a kan biyan hakkokin ‘yan wasan Super Eagles domin Shugaba Tinubu ya amince da duk wani abu da aka rubuta domin biyan ‘yan wasan,
Sai dai ya bukaci a ci gaba da yi musu addu’o’i na musamman domin ganin sun ‘yan wasan sun lashe gasar.