Babban Lauyan tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya umarci Ƴansandan Nijeriya da su miƙa kundin shari’ar masu zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gurfanar a babbar Kotun tarayya da ke Abuja zuwa ofishinsa.
Wannan ya biyo bayan wani lamari ne a jiya Juma’a, inda wasu daga cikin matasa masu zanga-zangar su biyar, da yawansu yara ‘yan ƙasa da shekara 15, suka yanke jiki sun fadi a kotu. Yayin sauraron shari’ar, mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da belin yara 67 da kuɗin jingina na miliyan N10 kowannensu tare da wani jami’in gwamnati a matsayin mai tsaya musu, yayin da sauran masu shekaru sama da 18 su 87 suma aka gurfanar da su.
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
- Yajin Aikin Ma’aikatan NAFDAC Ya Kazanta Halin Da Masana’antun Harhada Magunguna Ke Ciki
A cikin wata sanarwa, Fagbemi ya bayyana buƙatar duba kundin shari’ar, inda ya ce, “Na samu labari cewa ‘yansanda sun gurfanar da waɗanda aka kama dangane da zanga-zangar tashin hankali ta #EndBadGovernance a kotu da tuhume-tuhume da suka haɗa da cin amanar kasa.” Ofishin AGF zai duba kundin domin yiwuwar sauya da ranar sauraron shari’ar, wadda aka tsayar zuwa watan Janairu.
Fitattun mutane sun yi Allah wadai da yadda ake tsare da yaran da ake tuhuma, suna kira ga a ba su kulawa mai kyau da ɗaukar matakan ladabtarwa cikin kwarewa.