Farfesa Umaru Pate, Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK), ya bayyana cewa sama da ayyuka miliyan 92 za su bace a duniya cikin shekaru biyar masu zuwa saboda tasirin fasahar ƙirƙirar basira (Artificial Intelligence (AI).
Ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na 6 zuwa 9, inda ya ce duk da cewa sabbin fasahohi za su samar da sabbin ayyuka, sai waɗanda suka dace da sabbin ƙwarewa da tunani za su iya cin moriyarsu. Ya ce rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa sabbin ayyuka miliyan 120 za su ɓullo, musamman ta hanyar AI, na’urorin saƙago (robot) da bayanai masu yawa.
- Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano
- 2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega
Farfesa Pate ya buƙaci jami’o’in Nijeriya da su daina koyar da ɗalibai abubuwan da ba su da amfani a duniya ta zamani. A cewarsa, lokaci ya yi da za a sauya tsarin koyarwa zuwa wanda ya dace da fasahar zamani da AI.
Ya ce arziƙin zamani ba ya dogara da mai ko albarkatu, sai dai ilimi da kirkire-kirkire. Don haka, jami’o’i su ɗauki nauyin sauyi ta hanyar gina cibiyoyin bincike masu inganci, ɗakunan gwaje-gwaje da kuma dabarun kasuwanci da za su tallafa wa cigaban ƙirƙire-ƙirƙire.
Ya jaddada buƙatar ƙara zuba jari a ilimin matasa, inda ya bayyana cewa su ne makomar ci gaban ƙasa. Ya buƙaci ɗaliban da aka yaye da su mai da hankali wajen samun sabbin fasahohin kwamfuta da tunani mai zurfi, domin su kasance cikin waɗanda za su tsira a zamanin da muke ciki. Ya yaba da lakcar da Farfesa Muhammad Ali Pate ya gabatar kafin bikin, wacce za a saka cikin sabon tsarin kwalejin lafiya na jami’ar.
A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta karrama mutane biyar da digirin girmamawa saboda gudummawarsu ga ci gaban kasa da ilimi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp