Aikin gina bututun gas tsakanin Nijeriya da Morocco ya kai wani sabon mataki bayan tarukan kwamitin fasaha da na jagoranci da aka gudanar a Rabat, babban birnin Morocco. Wannan gagarumin aiki wanda zai ratsa ƙasashe 13 na Afrika, an tsara shi ne domin isar da iskar gas daga Nijeriya zuwa Turai ta bakin tekun yammacin Afrika, tare da amfanar ƙasashen da bututun zai ratsa.
Sanarwar da Hukumar Harkokin Ma’adanai da Man Fetur ta Morocco (ONHYM) ta fitar ta bayyana cewa an kammala binciken fasaha da na tasirin muhalli a sashin arewa na bututun, yayin da ake ci gaba da irin wannan bincike a sashin kudu daga Nijeriya zuwa Senegal. Har ila yau, an kafa kamfanin da zai jagoranci aikin (Holding Company), tare da ƙirƙirar ƙananan kamfanoni (SPVs) don kula da kowane sashi na aikin.
- Hukumar CAF Ta Sanar Da Garuruwan Da Za A Buga Gasar AFCON 2025 A Morocco
- Morocco Za Ta Sake Karbar Bakuncin WAFCON A 2026
A lokacin taron da aka gudanar a Rabat a ranar 10 da 11 ga Yuli, kamfanonin NNPC daga Nijeriya, ONHYM daga Morocco da SOTOGAZ daga Togo sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya, wacce ta tabbatar da aikin shiga Togo cikin. Wannan mataki ya kammala haɗin gwuiwa tsakanin dukkan ƙasashen da bututun zai ratsa.
Bututun zai fara daga Nijeriya, ya wuce ta ƙasashen Benin, Togo, Ghana, Côte d’Ivoire, Liberia, Sierra Leone, Guinea, Guinea-Bissau, Gambia, Senegal, da Mauritania kafin ya isa Morocco. Daga nan kuma, zai haɗu da bututun Maghreb-Europe da hanyoyin iskar gas na Turai, tare da samar da gas ga ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
Wannan aikin, wanda aka fara ƙarƙashin jagorancin Sarkin Morocco Mohammed VI da Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, yana da nufin ƙarfafa haɗin kai, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasashen Afrika. Ana sa ran aikin zai zama jigo wajen inganta rayuwar al’ummomi, da haɓaka amfani da makamashi mai tsafta, da ƙarfafa haɗin gwuiwar yankin Atlantic.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp