Mahukuntan kasar Saudiyya sun karrama gwamnatin Jihar Sakkwato da babbar lambar yabo bisa yadda gwamnatin jihar ta samu nasarar gudanar da ayyukan aikin hajji na 2024 da aka kammala.
Shugaban hukumar jin dadin alhazai Jihar Sakkwato, Aliyu Musa ne ya mika lambar yabon ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, a gidan gwamnatin jihar.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- DSS Ta Musanta Kai Samame Ofishin NLC Kan Zanga-zangar Yunwa
Musa ya shaida wa gwamnan cewa, Saudiyya ta karrama gwamnatin jihar da babbar lambar yabon ne saboda yadda tun da farko, gwamnatin jihar ta yi gagarumin shiri wajen kula jin dadi da walwalar alhazanta aikin hajjin bana da aka kammala.
A jawabinsa a lokacin da ya karbi babbar lambar yabon, Gwamna Aliyu, ya jinjina wa jami’an hukumar na jihar, bisa namijin kokarin da suka yi har ta kai ga gwamnatin jihar ta samun nasara a lokacin gudanar da aikin hajjin bana.
“Ina yi maku godiya bisa wannan namijin kokarin da kuka yi a lokacin gudanar da ayyukan hajjin bana, tabbas abin yabawa ne matuka.”
A cewarsa, ciyar da alhazan jihar da gwamnatin jihar ta yi a Saudiyya a lokacin aikin hajjin bana, ba za a iya kwatantawa da na wasu jihohin ba, saboda haka, ku ci gaba da yin aiki mai kyau.
Kazalika, Aliyu ya bai wa hukumar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa hukumar domin ta ci gaba da samun nansara a aikin hajji da ke tafe.
Tun da farko a jawabinsa, shugaban hukumar ya gode wa gwamnan bisa bai wa hukumar dukkan wani goyon baya da ta bukata domin ta gudanar da aikin hajji a cikin nasara.
Shugaban ya kuma bai wa gwamnan tabbacin cewa shi da jami’ansa za su ci gaba da yin aiki tukuru, musamman domin su sauke nauyin da aka dora masu.