ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Aikin Maɗaciya A Jikin Ɗan’adam

by Sani Anwar
5 months ago

Jakar maɗaciya na nan ɗanfare da hanta, daga ƙasan hantar a ɓangaren dama daga sama a cikin Ɗan’adam.Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya, wadda ke da launin kore ko kuma rawayar gwal, sannan sai ruwan maɗaciyar ya gangaro zuwa cikin jakar maɗaciya; domin ajiya zuwa lokacin da za a buƙace shi.

Kazalika, Hanta na iya samar da ruwan maɗaciya da yawansa ya kai kimanin lita 800 zuwa 1200 a kullum. A yayin da jakar maɗaciyar ke iya cin ruwan maɗaciyar da yawansa ya kai lita 50 bayan ta tace mafi yawan ruwan da ke ciki.

  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Har ila yau, ruwan maɗaciya ya ƙunshi kashi 97.6 cikin 100 ruwa zalla da kuma kashi 2.4 cikin 100 na gishirin maɗaciya da sauran ɓurɓishin ma’adanai da sauran makamantansu.

ADVERTISEMENT

Gishirin maɗaciya shi ne jigon aikin maɗaciya a jikin Ɗan’adam, musamman wajen narka abinci da mutum ya ci.

Haka zalika, gishirin maɗaciya shi ne jigon sinadarin da ke narka ko markaɗa abinci a ajin mai ko kitse a cikin ƙaramin hanji, har a mayar da shi zuwa yadda jiki zai iya zuƙar sa daga ƙaramin hanji zuwa sassan jiki. 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

Bugu da ƙari, gishirin maɗaciya na taimakawa wajen yi wa hanta ƙaimi; don samar da ruwan maɗaciya a jikin mutum.

Har wa yau, gishirin maɗaciya na taimakawa wajen sauƙaƙa fitowar bayan-gida daga cikin babban hanji zuwa dubura. Haka kuma, daga cikin ruwan maɗaciyar ne bayan-gida ke samun launi irin na ruwan ƙasar da yake da shi.

Tsakuwar maɗaciya: A yayin da kwalastirol ko kitse ya yi yawa a jikin mutum, kwalastirol ɗin na iya curewa wuri guda ya haifar da matsalar da ake cewa; tsakuwar maɗaciya wato ‘gallstone’ a turance. Gishirin maɗaciya na taimakawa wajen magance curewar kwalastirol a cikin jakar maɗaciyar da ke jikin Ɗan’adam.

Haka zalika, duk da ɗimbin alfanun da maɗaciya ked a shi a jikin Ɗan’adam, ana iya yin tiyata a cire jakar maɗaciyar idan aka samu matsalar tsakuwar maɗaciya; sannan kuma a gaza samun magungunan da za su magance cutar tsakuwar.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
Kiwon Lafiya

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

August 29, 2026
Next Post
Hanyoyin Da Ya Kamata Abi Don Gyaran Jiki?

Hanyoyin Da Ya Kamata Abi Don Gyaran Jiki?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.