ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Ya Kamata Abi Don Gyaran Jiki?

by Bilkisu Tijjani
5 months ago

A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kuɗi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kuɗin sayan kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada ɗaya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki.

Idan ana so a gyara gashi za a iya haɗa Ayaba da Ƙwai sai a kwaɓa su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.

Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matuƙar kyau sosai.

ADVERTISEMENT
  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan ɗumi. A gwada wannan haɗin sau ɗaya ma a sati za a ga canji.

Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke maƙale a gefen gashin kai.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka baƙin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.

Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaɓa sai a riƙa dirzawa a fatar jiki a ƙalla sau uku a sati.

Man kwakwa na matuƙar gyaran zubewar gashin kai. Za a iya shafa man kwakwa a fatar kai, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa ɗaya sannan a wanke.

Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwakwa,  yana gyarawa ya yi baƙi, sheƙi da gyalli.

A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a riƙa shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.

Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.

Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
An Cafke Ɗalibai 6 A Kogi Bisa Zargin Kai Hari A Harabar Makaranta

An Cafke Ɗalibai 6 A Kogi Bisa Zargin Kai Hari A Harabar Makaranta

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.