Wata mata mai yara biyu, Aisha Suleiman, ta bayyana yadda ita da ’ya’yanta, ciki har da jaririnta da aka haifa kwanan nan, suka tsira daga gobarar da ta ƙone gidaje uku a yankin Oloje Phase II da ke birnin Ilorin, Jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na daren Talata, 27 ga Oktoba, 2026, lokacin da Aisha ta farka bayan ta ji wani sautin wutar lantarki daga ƙarƙashin firij ɗinta. Da ta duba, sai ta ga wuta ta kama ƙarƙashin firij ɗin. Ta tada mahaifiyarta, sannan ta yi ƙoƙarin kashe gobarar ta hanyar amfani da ruwa da sabulu, amma abin ya ci tura yayin da wutar ke ƙara yaɗuwa. Aisha ta ce daga ƙarshe ta ɗauki muhimman takardunta, ta fitar da silindar iskar gas ɗinta, sannan ta ɗauki ’ya’yanta biyu suka tsere daga gidan.
Ta bayyana cewa gobarar ta lalata kusan dukkan kayayyakin gidanta, ciki har da kujeru, da firiji, da kayan ɗakunan ajiya, da janareta da sauran kayan girki. Ta kuma koka kan matsalar rashin wutar lantarki da mazauna unguwar ke fuskanta, inda ta ce sun shafe kusan shekaru uku suna fama da matsalar lantarki. A cewarta, an kuma samu wani abin da ya shafi wutar lantarki a unguwar kimanin makonni biyu kafin aukuwar gobarar.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda jami’inta mai magana da yawun hukumar, Hassan Adekunle, ya ce sun samu kiran neman agaji da ƙarfe 2:41 na dare, inda suka isa Lawyer Lambo Street da ke Ƙaramar Hukumar Ilorin West. Gobarar ta shafi gine-gine uku, ciki har da gidaje biyu masu ɗakuna huɗu-huɗu da wani ƙaramin gida mai ɗaki da falo. Motoci uku ne suke a ɗaya daga cikin gine-ginen, amma gobarar ta ƙone guda ɗaya, yayin da jami’an kashe gobara suka yi nasarar ceto sauran biyun. Haka kuma, gobarar ta lalata wani shagon gyaran tayoyi da ofishin kamfanin yawon buɗe ido.
Hukumar ta ce binciken farko ya nuna cewa rushewar wani siminti da ke riƙe da layin wutar lantarki mai ƙarfin 33kV ne ya haddasa lamarin. Wayar wutar da ta faɗo ta taɓa motar da ta ƙone, inda tartsatsin wuta ya kama tayarta kafin gobarar ta bazu. Saboda haɗarin wayoyin lantarkin da suka faɗo, hukumar kashe gobarar ta tuntubi kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC) domin katse wutar lantarkin yankin kafin jami’anta su ci gaba da aikin kashe gobarar.
Shugaban hukumar kashe gobarar jihar, Alabi Muhammed, ya jajantawa waɗanda abin ya shafa, tare da gargaɗin jama’a kan gina gidaje ko wasu gine-gine a ƙarƙashin manyan layukan wutar lantarki. Ya kuma bukaci mazauna yankunan da su riƙa kai rahoton turaken lantarkin da suka faɗo, ko wayoyin lantarki da suka lalace ko suka buɗe ga hukumomin da abin ya shafa, tare da guje wa taɓa wayoyin lantarki da suka faɗo.














