ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Mulkin Buhari Da Na Tinubu, Wanne Mutane Suka Fi Samun Walwala?

by Sulaiman and Sani Anwar
5 hours ago
Buhari

Muhawararmu ta wannan makon, ta karkata ne kan jin ra’ayoyin masu karatu, dangane da mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu, shin a tsakanin mulkinsu, wanne mutane suka fi samun walwala? SANI ANWAR da MUHAMMAD BAkIR ne, suka tattaro ra’ayoyin naku.

Ridwan Nuhu Mukhtar

Idan muka yi la’akari da walwalar talakan Nijeriya ta fuskar farashin abinci, fetur, sufuri da karfin sayen kudi, zamanin Buhari ya kasance da wasu saukakan yanayi fiye da farkon mulkin Tinubu, musamman saboda ci gaba da tallafin man fetur.Amma Buhari ma ya bar manyan matsalolin tattalin arziki, ciki har da faduwar naira, hauhawar farashi da rashin aikin yi.

ADVERTISEMENT

Saboda haka, ba za a iya cewa Buhari ya magance matsalolin tattalin arzikin kasa ba. Abin da za a iya cewa shi ne, talaka ya fuskanci matsin tsadar rayuwa mafi tsanani a farkon mulkin Tinubu.

Abdulmalik B. Muhammad

LABARAI MASU NASABA

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa

Tsakanin Talauci Da Jahilci Wanne Ya Fi Jefa Matasa Mummunar Hanya?

 Idan aka kwatanta mulkin Buhari da na Tinubu ta fuskar walwalar talaka, a zamanin Buhari mutane sun fi samun sauki a wasu abubuwa, musamman farashin fetur da sufuri saboda tallafin gwamnati. Amma a zamanin Tinubu, cire tallafin fetur da sauye-sauyen tattalin arziki, sun kara wa jama’a nauyin rayuwa.Duk da cewa, Tinubu ya kara albashi daga naira 30,000 zuwa 70,000, tsadar abinci da sauran bukatun yau da kullum, sun rage amfanin wannan karin albashi.

Babban abin fahimta shi ne: ingancin mulki ba a auna shi da yawan kudin da gwamnati ke samu, ana auna shi ne da yadda rayuwar talaka take inganta.

Sadik Suleiman

Bambancin mulkin Buhari da Tinubu shi ne, a zamanin Buhari an fi samun sauki wajen biyan wasu bukatun yau da kullum saboda tallafin man fetur, duk da matsalolin tattalin arziki da aka fuskanta. A zamanin Tinubu kuwa, an aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki wadanda suka kara tsadar rayuwa ga jama’a.Abin takaici shi ne, karin albashi ba ya wadatarwa idan farashin abinci, haya da sufuri na ci gaba da tashi.

Gwamnati mai inganci ita ce wadda manufofinta ke saukaka rayuwar talaka, ba wai kawai wadanda ke inganta alkaluman tattalin arziki ba.

Yusuf Muhammad

A nawa ganin, al’umma sun fi samun walwala a lokacin mulkin Buhari, idan aka kwatanta da na Tinubu, domin duk da cewa; matsin rayuwa ya fara kamari ne a zamanin Buhari, a mulkin Tinubu kuma abubuwa sun kara tsananta.Sai dai kuma, Tinubu ya bayyana cewa; zai dora ne daga inda Buhari ya tsaya. Don haka, ba za a iya tabbatar da cewa da Buhari ya ci gaba da mulki abubuwa ba za su kara lalacewa fiye da na Tinubu ba.

Abdullahi Umar

Magana ta gaskiya, an fi samun sauki tare da walwala a mulkin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari fiye da mulkin Shugaba Tinubu. Abubuwa da dama da suka hada da; tattalin arziki, tsaro da samun saukin rayuwa, sun dan fi dama-dama a lokacin Buhari, duk da cewa; da ma Tinubu ya bayyana cewa; zai dora ne a kan mulkin Buhari.

Amma fa batu na samun walwala, ‘yan Nijeriya ko kadan ba su samu yadda suke so ba, a karkashin mulkin APC kwata-kwata, idan ban da wahala da yunwa da matsalar rashin tsaro. Da Buhari da Tinubu, danjuma ne da danjummai ta fuskar rashin iya jagoranci da tausaya wa al’ummar da suke jagoranta. Wannan dalili ne ya kawo mu wannan hali na kunci da wahalhalu da muke ciki.

Safiyya Rabiu Ali Indabawa

A iya cewa mulkin Tinubu kamar ya fi dama-dama a kan na Buhari, koda-yake danjuma ne da danjummai, kuma ba wai na fada ne don ina son Tinubu ba, sai don wasu dalilai kamar haka:

Idan muka duba bangaren tsaro, a mulkin Buhari aka fara garkuwa da mutane, sannan a cikinsa ne aka rufe kan iyakokin Nijeriya har ta kai ga ana kashe mutane idan sun shigo da shinkafa daga waje, an hana shigo da shinkafa amma ba a hana shigo makamai ba, mutane sun ci ganyen Tafasa a zamaninsa wanda a yanzu ba a cin wannan kanye na Tafasa kwata-kwata a iya sanina. Sannan duk wannan yunwa da ake fama da ita a halin yanzu, shirin Buhari ne, kawai Tinubu ya zo ya dora ne, domin da kansa Buhari ya ce; idan ya sauka sai an ce gara mulkinsa da wanda zai zo nan gaba, ashe dama akwai wata kullalliya a kasa kenan. Ni wannan shi ne dalilina, sai dai kuma, ba na ra’ayin Tinubu kuma ba zan zabe shi ba, illa dai kawai na fadi gaskiya ne ko iyakar abin da na fahimta.

Buhari
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    CMG Da MDD Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna
  • Sulaiman
    Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Yin Kokari Wajen Gina Al’ummar Asiya Da Tekun Fasifik”
  • Sulaiman
    Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Balaguron Fasinjoji Sau Biliyan 4.13 A Cikin Watanni 10 Na Farkon 2026
  • Sulaiman
    Shugabanni 12 Na Yankunan Tattalin Arzikin Kungiyar APEC Za Su Halarci Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na 2026
Buhari
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shirin Sulhu Tsakanin Kwankwaso Da Abba: Ina Aka Dosa?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

MASU ALAKA

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa
Taskira

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa

October 11, 2026
Yarjejeniyar Zaman Lafiya
Taskira

Tsakanin Talauci Da Jahilci Wanne Ya Fi Jefa Matasa Mummunar Hanya?

October 4, 2026
Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

LABARAI MASU NASABA

CMG Da MDD Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna

CMG Da MDD Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna

November 15, 2026
Ƙasar Italiya Ta Ci Tarar Facebook Yuro Miliyan 805

Ƙasar Italiya Ta Ci Tarar Facebook Yuro Miliyan 805

November 15, 2026
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Yin Kokari Wajen Gina Al’ummar Asiya Da Tekun Fasifik”

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Yin Kokari Wajen Gina Al’ummar Asiya Da Tekun Fasifik”

November 15, 2026
Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Balaguron Fasinjoji Sau Biliyan 4.13 A Cikin Watanni 10 Na Farkon 2026

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Balaguron Fasinjoji Sau Biliyan 4.13 A Cikin Watanni 10 Na Farkon 2026

November 15, 2026
Shugabanni 12 Na Yankunan Tattalin Arzikin Kungiyar APEC Za Su Halarci Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na 2026

Shugabanni 12 Na Yankunan Tattalin Arzikin Kungiyar APEC Za Su Halarci Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na 2026

November 15, 2026
Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

Ƴan Bindiga Sun Harbe Hadimin Gwamnan Zamfara Har Lahira

November 15, 2026
Da Mulkin Buhari Da Na Tinubu, Wanne Mutane Suka Fi Samun Walwala?

Da Mulkin Buhari Da Na Tinubu, Wanne Mutane Suka Fi Samun Walwala?

November 15, 2026
Dangote Ya Ƙarfafa Zuba Jari A Fanni Gona, Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Kayan Gona Na 2026

Dangote Ya Ƙarfafa Zuba Jari A Fanni Gona, Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Kayan Gona Na 2026

November 15, 2026
Atiku: An Dakatar da Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Jam’in Da Muka Yi

Atiku: An Dakatar da Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Jam’in Da Muka Yi

November 15, 2026
Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Kannywood Makon Da Ya Gabata

Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Kannywood Makon Da Ya Gabata

November 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.