A taron majalisar ministoci da gwamnatin tarayya ta saba yi Ministar Mata, Hajiya Aisha Alhassan ta halarci zaman majalisar a yau Laraba, tare da sauran ministocin.
Aisha, ta samu kyakkyawar tarbo daga sauran ministoci da suka halarci zaman sabanin yadda ake tunanin ministocin za su iya juya mata baya bisa fadar ra’ayinta da ta yi na nuna goyon bayanta ga takarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a makon da ya gabata.
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar da misalin Karfe 11:00.