Ayayin da ake shirin bikin ranar zaman lafiya da addu’a ta duniya na ranar 21 ga watan Yuni 2022, akalla malamai dari (100) da suka hada da musulmi da kiristoci daga jihohin arewacin Nijeriya ne suka hadu, yayin da wasu suka gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da hadin kai a wuraren ibadarsu da ya gudana a Jihar Kaduna.
Malaman sun bayyana cewa Allah ya nufe su ne da su yi magana a madadin wadanda ba za su iya yin magana da kansu domin bukatar dorewar zaman lafiya, fahimtar juna, hakuri da afuwa a tsakanin kungiyoyi addinai daban-daban.
Da yake bayani babban mai kula da cocin ‘Christ Evangelical and life intervention ministry’, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa akwai bukatar yin hakan ranar bikin wannan shekara na zaman lafiya da addu’o’i ta duniya.
A cewarsa, kungiyar fastoci da ‘yan’uwa a fadin kasar nan wadanda suka hada da kungiyarsa ta (Peace Revival and Recounciliation Foundation of Nigeria) na da bukatar a fara gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar domin babban zabe na 2023 mai zuwa.
Ya ce a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, dukkan masu neman kujerar sanata, gwamna da shugaban kasa na bukatar addu’o’in neman tsarin Allah da nasara, don haka akwai bukatar dukkanin malaman addini su shirya addu’a ga ‘yan takara ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasarsu ba.
Ya ce “Muna addu’ar Allah ya ba su hikima ta yadda za su wakilci kowa a kasar nan ba tare da la’akari da al’adu, addini, yanki, da dai sauransu ba”
“Ya Ubangiji, ka ba shugabanninmu hikima domin su yi abin da ya fi karfin fahimtarsu.
Ka taimakesu su zabi hanyar da ta dace a lokacin da suke yanke shawara a madadin wannan al’umma.”
Da yake mayar da jawabi, Malam Mohammed Sani, daya daga cikin Malaman addinin Musulunci na Kaduna ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su rika yi wa shugabansu addu’a.
Ya kara da cewa yana da kyau kowane dan kasa ya rika mara wa shugabansa baya da addu’o’i masu kyau, domin Allah ya taimake shi ya sauke nauyin da yake kansa.
Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da ‘yan daba a lokacin yakin neman zabe.