• Leadership Hausa
Sunday, August 14, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Rahotonni

Akalla Malamai 100 Daga Arewacin Nijeriya Suka Yi Addu’ar Samun Nasarar Zaben 2023

by Sulaiman and Shehu Yahaya
2 months ago
in Rahotonni
0
Rabi Shehu Sharada: ‘Yan Siyasa Sun Ci Moriyar Ganga, Sun Yada Kwaurenta!
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ayayin da ake shirin bikin ranar zaman lafiya da addu’a ta duniya na ranar 21 ga watan Yuni 2022, akalla malamai dari (100) da suka hada da musulmi da kiristoci daga jihohin arewacin Nijeriya ne suka hadu, yayin da wasu suka gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da hadin kai a wuraren ibadarsu da ya gudana a Jihar Kaduna.

Malaman sun bayyana cewa Allah ya nufe su ne da su yi magana a madadin wadanda ba za su iya yin magana da kansu domin bukatar dorewar zaman lafiya, fahimtar juna, hakuri da afuwa a tsakanin kungiyoyi addinai daban-daban.

  • 2023: INEC Ta Kafa Sharuda Biyu Ga jam’iyyun Da Ke Son Sauya Abokan Takara

Da yake bayani babban mai kula da cocin ‘Christ Evangelical and life intervention ministry’, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa akwai bukatar yin hakan ranar bikin wannan shekara na zaman lafiya da addu’o’i ta duniya.

A cewarsa, kungiyar fastoci da ‘yan’uwa a fadin kasar nan wadanda suka hada da kungiyarsa ta (Peace Revival and Recounciliation Foundation of Nigeria) na da bukatar a fara gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar domin babban zabe na 2023 mai zuwa.

Ya ce a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, dukkan masu neman kujerar sanata, gwamna da shugaban kasa na bukatar addu’o’in neman tsarin Allah da nasara, don haka akwai bukatar dukkanin malaman addini su shirya addu’a ga ‘yan takara ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasarsu ba.

Labarai Masu Nasaba

Mata A Daina Yawace-yawace Da Shige-shige Mara Amfani -Halima Kassim

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

Ya ce “Muna addu’ar Allah ya ba su hikima ta yadda za su wakilci kowa a kasar nan ba tare da la’akari da al’adu, addini, yanki, da dai sauransu ba”
“Ya Ubangiji, ka ba shugabanninmu hikima domin su yi abin da ya fi karfin fahimtarsu.

Ka taimakesu su zabi hanyar da ta dace a lokacin da suke yanke shawara a madadin wannan al’umma.”
Da yake mayar da jawabi, Malam Mohammed Sani, daya daga cikin Malaman addinin Musulunci na Kaduna ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su rika yi wa shugabansu addu’a.

Ya kara da cewa yana da kyau kowane dan kasa ya rika mara wa shugabansa baya da addu’o’i masu kyau, domin Allah ya taimake shi ya sauke nauyin da yake kansa.

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da ‘yan daba a lokacin yakin neman zabe.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mamaki Ya Cika Ango Da Amarya Kan Yadda Suka Kwana Da Bakon Kare

Next Post

Sharhi: Ko INEC Za Ta Samu Nasarar Sahihin Zabe A 2023?

Related

Mata A Daina Yawace-yawace Da Shige-shige Mara Amfani -Halima Kassim
Rahotonni

Mata A Daina Yawace-yawace Da Shige-shige Mara Amfani -Halima Kassim

12 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja
Rahotonni

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

2 days ago
Tsadar Farashi: Yadda ‘Yan Nijeriya Suka Koma Sayen Kaya Masu Araha
Rahotonni

Tsadar Farashi: Yadda ‘Yan Nijeriya Suka Koma Sayen Kaya Masu Araha

2 days ago
Yaki Da Safarar Mutane A Duniya
Rahotonni

Yaki Da Safarar Mutane A Duniya

2 days ago
Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Jita-jitar Malalar ‘Yan Ta’adda Tsakanin Kaduna Da Zariya
Rahotonni

Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Jita-jitar Malalar ‘Yan Ta’adda Tsakanin Kaduna Da Zariya

3 days ago
Shugaban NIS Ya Yi Gargaɗin Biyan Kuɗin Fasfo Da Tsabar Kuɗi A Hannu
Rahotonni

Shugaban NIS Ya Yi Gargaɗin Biyan Kuɗin Fasfo Da Tsabar Kuɗi A Hannu

4 days ago
Next Post
Sharhi: Ko INEC Za Ta Samu Nasarar Sahihin Zabe A 2023?

Sharhi: Ko INEC Za Ta Samu Nasarar Sahihin Zabe A 2023?

LABARAI MASU NASABA

An Bukaci Al’umma Su Ci Gaba Da Gudanar Da Addu’o’in Neman Zaman Lafiya

An Bukaci Al’umma Su Ci Gaba Da Gudanar Da Addu’o’in Neman Zaman Lafiya

August 13, 2022
EFCC Ta Cafke Malaman Addini 2 Da Wasu 5 Kan Zargin Damfara A Yanar Gizo A Kwara

EFCC Ta Cafke Malaman Addini 2 Da Wasu 5 Kan Zargin Damfara A Yanar Gizo A Kwara

August 13, 2022
Fiye Da Miliyan 326 Muka Biya Ma’aikata Da Suka Yi Ritaya A Shekarar Bara -Hukumar Fansho

Fiye Da Miliyan 326 Muka Biya Ma’aikata Da Suka Yi Ritaya A Shekarar Bara -Hukumar Fansho

August 13, 2022
Ganduje Ya Nada Shugabannin Gudanarwa Da Mambobin Hukumar Shari’a

Ganduje Ya Nada Shugabannin Gudanarwa Da Mambobin Hukumar Shari’a

August 13, 2022
Akwai Babban Aiki A Gaban Erik ten Hag A Man U

Akwai Babban Aiki A Gaban Erik ten Hag A Man U

August 13, 2022
Jakadan Kasar Sin Dake Nijar Ya Gana Da Tsohon Shugaban kasar

Jakadan Kasar Sin Dake Nijar Ya Gana Da Tsohon Shugaban kasar

August 13, 2022
Damfarar Miliyan 66: Kotu Ta Daure Maman Boko Haram Da Wasu Mutum 2

Damfarar Miliyan 66: Kotu Ta Daure Maman Boko Haram Da Wasu Mutum 2

August 13, 2022
Wacce Kungiya Za Ta Lashe Firimiyar Ingila?

Wacce Kungiya Za Ta Lashe Firimiyar Ingila?

August 13, 2022
Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Gudunmawar Naira Biliyan 2.5 Don Kammala Aikin Tashar Tsandauri

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Gudunmawar Naira Biliyan 2.5 Don Kammala Aikin Tashar Tsandauri

August 13, 2022
Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye Ne, Saurayi Ko Budurwa?

Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye Ne, Saurayi Ko Budurwa?

August 13, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.