Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya fara bincike kan likitan da ya yi sakacin ruvewar hannun jariri tare da yin Allah wadai da lamarin.
Wannan na zuwa ne bayan da gidan rediyon Premiere FM da ke Jihar Kano ta bankado labarin yadda ake zargin likitan da sakacin ruvewar hannun jaririn.
- 2023: INEC Za Ta Dauki Ma’aikata Miliyan 1.4 Domin Horar Da Su Fasahar BVAS – Okoye
- Yadda Sakacin Likita Ya Jawo Rubewar Hannun Jariri A Kano
Premier Radio ta gano cewa sakacin ya faru ne tun ranar da aka haifi jaririn, bayan an yi tiyatar ciro shi.
Hukumar asibitin ta Aminu Kano a cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Laraba mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Asibitin Hauwa Muhd Abdullahi, ta ce asibitin ya girgiza matuqa da jin wannan mugun labari.
Asibitin ya ce a cikin shekaru 33 da kafuwar asibitin hakan bai tavar faruwa ba, kuma hukumar gudanarwar asibitin na jajantawa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru.
Bugu da qari, tuni asibitin ya mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badaqala da sakacin aiki domin zurzurfafa bincike tar da xaukar matakin da ya dace.