Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi ‘yan kasa na kimanin kwanaki 30 duk da cewa an fara ganin dogayen layukan mai tun da maraicen ranar Litinin.
Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta ce tabbas an fara ganin dogayen layukan mai kuma hakan baya rasa nasaba da furucin shugaba Tinubu amma sai mambobinta sun sayo mai daga NNPCL din a yau kafin ta iya magana a kan batun karin farashin da za a iya gani, lamarin da ya fara sanya fargaba a zukatan ‘yan Nijeriya.
- Daga Karshe Dai, Cire Tallafin Mai Ya Tabbata, NNPC Na Sayar Da Lita N537 A Abuja
- Burina Tinubu Ya Tilasta Wa Maza Kara Aure —Rashida Mai Sa’a
Jim kadan bayan ayyana janye tallafin man fetur da sabon shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabinsa bayan rantsar da shi ne, aka fara ganin dogayen layukan mai a birnin tarayya Abuja da wasu sassan kasar na duk da cewa ‘yan kasar nan sun yi marhaban da matakin da Tinubun ya sanar a ranar Litinin din.
Tuni dai wasu ‘yan Nijeriya ma suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da lamarin inda wasu ke ganin cewa bai kamata a dora laifin dogayen layuka da aka fara gani a kan gwamnati ba illa ‘yan kasuwa ne suka fara boye man don cin kazamar riba wasu kuma ke cewa ‘yan kasa ne suke nuna fargabar sayen mai suna karfafa wa ‘yan kasuwa wajen boyewa.
A wani bangare kuwa, a cikin wata sanarwa da shugabanta Festus Osifo da babban sakatare, Nuhu Toro suka sanya wa hannu, kungiyar ma’aikatan kamfanoni ta Nijeriya (TUC) ta bayyana cewa sabon shugaban kasa Bola Tinubu ba zai iya daukar matakin cire tallafin man fetur shi kadai ba kuma kamata ya yi ya dakata na dan lokaci don ba da damar tattaunawa mai karfi da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki, kafin yanke shawara kan batun janye tallafin man fetur.
TUC ta kara da cewa akwai batutuwa da dama da ya kamata a yi la’akari da su cikin ruwan sanyi da kuma warware su kafin shugaban ya yanke irin wannan shawara.
Idan ana iya tunawa dai tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya sha jaddada cewa za a janye tallafin man fetur a watan Yunin da za a shiga kuma ya kara karfafa batun a watan Afrilun da ya gabata, kuma masana sun ce bai kamata batun cire tallafin da sabon shugaba Tinubu ya yi a jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun ya shammaci ‘yan kasar nan ba sai dai kamata ya yi gwamnatin ta dauki dukkan matakan da suka dace don kawo sauki ga talaka.