Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya sanar da cewa akwai wawaken gibin da ake da shi a bangaren aikin na noman zamani a kasar nan matuka.
Sai dai, ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya ya yin dukkan mai yuwuwa, domin ganin ta cike wannan gibin ta hayar samar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryen da suka kamata.
Ministan ya kuma jadda da cewa, rance da muke samu, zai iya kawai daukar nauyinTaraktocin noma 10,000,
Alhaji Sabo Nanono ya sanar da cewa, Ma’aikatar za ta fara gudanar da noman zamani a kananan hukimom 632 da ke Nijeriya, inda ya ci gaba da cewa, wannam tsarin zai taimaka wajen kara wadata Nijeriya da abinci mai dimbin ya wa, kara bunkasa tallain arzikin Nijeriya da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar.
Ministan ya sanar da hakan ne a kwanan baya lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Biniwe Dakta Samuel Ortom a ofishin sa dake a babban birinin tarayyar in his Abuja.
Nanono ya ci gaba da cewa, shirin ana sa ran zai hada da yin amfani da kimiyyar zamani, inda hakan zai kuma kara samar da kudaden shiga.
Ministan ya kuma bayyana cewa, shirin za a yi shine a kananan hukumomi 632 dake a daukacin fadin Nijeriya, inda ya kara da cewa, ko wacce karamar hukma daya, za a samar mata da cibiya, inda kuma ko wacce za ta samu sabuwar Taraktar noma, tare da samar da wajen adana Irin noma, takin zamani da sauran su.
Ya yi nuni da cewa, da wannan ne za a hada manoman da masana’antun sarrafa amfanin gona, musamman wadanda su ke a kananan hukumomi, inda ya ci gaba, dabarun yin noman na zamani, alummar da ke a kananan hukumomin ne za su ci gaba da lura da su, inda ya kuma bukaci kungiyoyi da daidaikun jama’a su kawo takardun neman yadda zasu kula da cibiyoyin, inda ya kara da cewa, Gwamnatin Tarayya za ta samar da dukkan kayan da ake bukata don aiwatar da shirin.
Ministan ya ci gaba da cewa, masu zuba jari a cibiyoyin watakilan ba za su wuce daga miliyan 5 ziwa miliyan 6 ba, amma sai sun kasance sun mallaki kadarorin da suka kai na naira miliyan 150 na tsawon shekaru 15.
A kan kudin shigar da za a samu a shirin, Ministan ya sanar da cewa, ga Taraktar noma daya da zata yi aiki, an kiyasta za a samu daga naira 60,000 zuwa naira 75,000 a kullum, inda hakan zai sa a samu kudin shiga a kullum kimanin naira 30,000 zuwa naira 40,000 a kullum bayan an kuma warware wasu kudaden da aka kashe, inda da wannan, cibiyoyin zasu dinga biyan Taraktar noma har zuwa daga shekara 6 zuwa 7, inda ya yi nuni da cewa, Taraktocin za su kai har tsawon shekaru 25.
Ministan ya kuma jaddada cewa, rance da mu ke samu, zai iya kawai daukar nauyin Taraktocin noma 10,000, inda ya yi nuni da cewa, gibin da ake dashi na yin aikin na noman zamani ya na da ya wa matuka.
Nanono ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya zata yi hadaka da Gwamnatin jihar Biniwe kan ko wacce karamar hukumar ta daya don suma su amafa da shirin.
A kan noman Waken Soya ya ce, muna yin kyakyawan dubi kan fannin yadda za a kara bunkasa shi da kuma kara samar da ayyukanyi, inda ya sanar da ya cewa, Nijeriya ta na samun kasuwar sa sosai, musammanna kasar China.
A nasa jawabin Gwamnan jihar Biniwe Dakta Samuel Ortom ya ce, ‘yan Nijeriya kalubalen da su ke fuskanta na tsaro ya kuma hada da rashin aikin yi, inda ya yi nuni da cewa, fannin noma kadai zai iya magance rashin aikin yi a Nijeriya, musamman a tsakanin matasa, inda kuma Ortom ya bai wa Ministan tabbacin gwamnatin sa na yin hadaka da Ma’aikatar sa.
Ya ce, jihar Biniwe na da fadin kasar yin noma da ta kai 35,000 sama da kashi 95 bisa dari per na fadin kasar jihar y kara da cewa, jihar Biniwe na da fadin kasar yin noma da ta kai 35,000 sama da kashi 95 bisa dari na fadin kasar jihar.