Wasu za su iya cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ce ta fi amfani da ‘yan wasa bakar fada a kasar Ingila, sannan akwai kungiyoyi irin su Fouthmouth da Leceister City wadanda duka suke amfani da bakaken ‘yan wasa.
Amma lokacin da Dr Clibe Chijioke Nwonka ya je Manchester domin ziyartar abokansa a ranar 28 ga Satumban 2002, ya hadu da muhimmin al’amari, domin kuwa ya kalli wasan kwallon kafa mai cike da tarihi.
- Wakilin Sin Ya Bukaci Sassan Somaliya Da Su Kara Azamar Warware Sabani Ta Hanyar Tattaunawa
- Tinubu Ya Samar Da Naira Biliyan 29 Don Gyara Hanyoyin Kasar Nan
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a wannan ranar ta kasance kungiyar kwallon kafa da ta yi amfani da ‘yanwasa tara bakaken fata daga cikin 11 a wasan Premier League kuma uku daga cikinsu, Thierry Henry, Nwankwo Kanu da Kolo Toure, kuma suna cikin wadanda suka jefa kwallo a raga a wasan da Arsenal ta doke Leeds United da ci 4-1.
A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, Dr Nwonka, wanda yanzu farfesa ne a Unibersity College London, ya bayyana cewa kwazonsu ya nuna tasirin wannan lokacin mai tarihi da kuma muhimmancin launin fata a duniya.
Dr Nwonka ya nuna rawar da kungiyar ta taka ga tarihin al’adun bakaken fata, a matsayin daya daga cikin editan littafin da aka wallafa mai taken “Black Arsenal,” wanda ya kunshi bayanai da hotunan wasu da suke ganin suna da alaka da kungiyar da ke Birnin Landan.
“Ni dan Birtaniya ne mai asali daga Nijeriya, kuma ina ganin ‘yan wasa bakaken fata da ‘yan wasan Afrika a kwallon Birtaniya yana da muhimmanci a gare ni,” in ji shi.
Wani bangare na littafin ya yi sharhin gudunmuwar Arsenal ga kwararar ‘yan wasa bakaken fata a gasar Premier da kuma samun magoya baya mata a filin kungiyar na Emirates.
Ya ce yana jin kullum akwai wani abu muhimmi, kan yadda bakaken fata ke da alaka da Arsenal kuma goyon bayan da kungiyar ke samu zai shafi harakokin yau da kullum na dimbin magoya bayan kungiyar, kuma an tabo wannan a cikin littafin.
Wenger da Afirka
Ian Wright, shi ne ya kasance mai farin jini ga dimbin magoya bayan Arsenal bakaken fata a shekarun 1990, saboda yunwarsa ta cin kwallaye sai dai ba dukkanin magoya bayan Arsenal za su amince da hotonsa a bangon littafin Black Arsenal ba, amma Dr Nwonka da sauran ‘‘yan Nijeriya, suna ganin akwai wani muhimmin dan wasa.
Sun tuna tawagar Nijeriya da ta lashe sarkar zinari a wasannin Olympics bayan doke Argentina a shekarar 1996, kuma dan wasa Nwanko Kanu ne ya zura kwallon da ta bayar da nasara a wasan kusa da karshe da Brazil.
An haifi Kanu a Jihar Imo, dan wasan ya koma Arsenal ne daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta Italiya a 1999 kuma zuwansa Arsenal yana da muhimmanci ga bakaken fata a duniya.
Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger, wanda ya yi fice wajen sayen ‘yan wasan Faransa da bakaken fata, tare da renon ‘yan wasa da dama a shekara 22 da ya shafe yana horar da Arsenal tsakanin 1996 zuwa 2018.
Wenger ya samu karbuwa da girmamawa kan tsarinsa na tafiyar aikinsa musamman lokacin da Arsenal ta lashe kofi a kakar wasa ta 2003 zuwa 2004, kuma irin wannan nasarar ce wani bangare na magoya baya suka koma goyon bayan Chelsea abokiyar gabar Arsenal a London, wadda ta yi fice zamanin Jose Mourinho lokacin da ya dauko ‘yan wasa bakaken fata kamar su Didier Drogba na Ibory Coast da dan wasan Ghana Michael Essien da kuma dan wasan tsakiya na Nijeriya John Obi Mikel.
Amma duk da nasarorin ‘yan wasa bakaken fata, har yanzu wariyar launin fata babbar matsala ce a filin wasa domin kuwa a shekarar 2021, bayan rashin nasara a wasan karshe a gasar cin kofin Turai ta Euro 2020, hannun Italiya, ‘yan wasa uku na Ingila – Bukayo Saka, Jadon Sancho da Marcus Rashford, sun fuskanci wariyar launin fata saboda sun barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.
An kama mutum 11, kuma Arsenal ta fitar da sanarwa tana nuna goyon baya ga dan wasanta Saka da sauran abokan wasansa na Ingila, sai dai an dade Saka yana fuskantar wariya, ciki har da lokacin da Arsenal ta sha kashi a hannun Nottingham Forest a bara.
Matsalar wariya ta kasance ruwan dare a dukkanin bangarori na kwallon kafa da aka fi bayar da rahoto a Ingila, kamar yadda alkalumman kungiyar yaki da wariyar launin fata ta duniya mai suna Kick It Out suka nuna.
A kakar bana, Arsenal ta yi bikin alakarta da Afirka ta hanyar samar da rigar ‘yan wasa da ke da launi irin na tutar kasashen nahiyar Afirka kuma Foday Dumbuya, dan asalin kasar Saliyo, shi ne ya tsara rigar kuma a Birnin Freetown aka dauki bidiyon tallan sabbin tufafin ‘yan wasan.
Dan wasa Bukayo Saka, iyayensa ‘yan Nijeriya ne da suka haife shi a Landan, kuma yanzu shi yake da farin jinin magoya bayan Arsenal, sannan dan wasan mai shekara 23 ya yi wa Arsenal wasanni 230 kuma ya dade yana adawa da nuna wariyar launin fata, har ila yau, yanzu shi ne kan gaba a bunkasar alakar Arsenal da bakaken fata a duniya.