Connect with us

ADABI

Al’amarin Fatima Danbarno Baiwa Ce Daga Allah – Abdullahi Maizare

Published

on

ABDULLAHI YAHAYA MAIZARE, wanda shi ne shugaban kamfanin Maizar Publishers & Printing Press ya fadi hakan ne a ranar Laraba 19/09/2018 a tattaunawar da suka yi da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, ADAMU YUSUF INDABO, jim kadan bayan da kamfanin ya karrama fasihiyar marubuciyar Fatima Ibrahim Danbarno da kambun girmamawa na ‘BEST WRITER 2018’.

Wakilin namu ya tambaye shi cewa: “Shin ko da me kuka yi la’akari da shi wajen ba Fatima Danbarno wannan kambu na Best Writer” Sai ya amsa da cewa: “To a gaskiya al’amarin Fatima baiwa ce daga Allah, saboda ta dade tana fada min za ta yi rubutu amma da yawa ana ganin kamar kawai wasa take yi. Amma cikin yardar Ubangiji da ta fara yin rubutun sai ga littattafanta sun matukar karbuwa, don a cikinsu babu wanda ba a yi reprinting dinsa an kara yi ba, duk da in za ta buga littafi tana buga Dubu Uku, Dubu Hudu har Dubu  Shida ma. Amma sai ka ga ana rububisa cikin kankanin lokaci sai ya kare. Na ga duk cikin marubutan da suke buga litafansu a kamfanina su sama da 800 ban samu marubuciyar da cikin kankanin lokaci littattafanta na karewa har a zo ana nema ba kamar ta, saboda tsananin iya rubutu da kuma dadin labaranta. Don ta kai cewa ni ma idan na zauna ina aikin littafinta sai na ji bana son tashi saboda ina so na ji shin ya labarin nan zai kare”

Ita dai Fatima Danbarno, marubuciya ce da a iya cewa ta shigo duniyar rubutu da kafar dama a shekara ta Dubu Biyu Da Sha Biyu (2012) da littafinta Kowa Ya Kwana Lafiya  ya zuwa yanzu ko ta wallafa littattafai da dama. Ita ma wakilinmu ya tattauna da ita kamar haka: Shin ko ya kika samu kanki da kika ji albishir din kamfanin MAIZAR ya zabe ki a matsayin best writer?

A gaskiya ni da ya fada min dariya kawai na yi, ban dauki maganar da gaske ba.  Amma daga baya da na zauna na yi nazari, a lokacin da ya kira ni yana min fada akan na rufe layin wayar da makaranta littafaina suke iya samuna, wanda tarin yabo ne daga bakinsa, sai na daina daukar maganar wasa. Saboda na san halinsa, idan labari bai yi dadi ba, a gaban marubuciyar zai kushe labarin, ya gaya mata gaskiya. Don haka sai na tsinci kaina cikin farin ciki sosai.

To shin ko wanne irin salon bayar da labari kike amfani da shi haka da cikin kankanin lokaci sunanki ya yi shuhura a cikin marubuta?

Kafin in zama marubuciya ai sai da na faara zama karanciya. To da na zo ina rubutu, sai ya zamana ina yawan ziyartar shagunan masu siyar da littafai, muna musayar kalamai da mata ‘yan uwana. Na sami ilmi sosai. Kuma duk kankantar mutum idan na fahimci ya san abinda ban sani ba, bana girman kai wajen jawo shi in yi masa tambaya. Don haka ni salona, ya yi dai-dai da irin salon da zamani ya zo da shi ne. Ko da kuwa labarina labarin kauye ne, ina iya bakin kokari in ga ban yi amfani da gundurarren salo ba. Sannan littafaina, ina daukar labarin da zai iya tsayawa mutum a rai ne, in yi amfani da shi, don bana son ka karanta min labari ka mance labarin.

Kafin wannan award din da kamfanin MAIZAR ya ba ki, wanne nasarori ki ka samu a harkar rubutu?

Award din nan shi ne na Biyu.. Amma wannan ya fi burge ni kwarai! Abin alfaharina ne, a ce yau ma’aikatan littafaina sun gano nayi zarra a shekarar nan. Award kuma idan aka baka ko wani iri ne, ana nufin karfafa gwiwa ce. Babbar nasarar da na samu a rubutu Malam Adamu, ba zai wuce jama’a ba. Ina son jama’a ina son in ga kowa nawa ne, duk da ba zai yuwu ba, amma iya bakin gwargwado ni kam na sami abinda nake so wato jama’a.

Mun ji irin tarin nasarorin da kika samu ta silar rubutu, to amma dai hakan bai hana kuma a samu wani kalubalen ba shi ma ta silar rubutun ko?

Akwai wani kalubale da na taba samu, ba zan mance ba. Wani Dakta ya karanta wani gejeren labarin da na rubuta, sai ya ce duk in da na ke sai an nemo ni. A lokacin da ake nemana ni kuma na koma Kaduna. Kai tsaye ya gabatar da kansa agun iyayena, ya ce shi aurena zai yi. A gaskiya duk a kalubalen da nake fuskanta wannan ya fi daga min hankali. Daga karshe ma na tsani rubutu, nace na daina yi, saboda abubuwa marasa dadi da suka yi ta faruwa. A lokacin da gaske na janye yin rubutun, na koma ko na zo yi sai bacin rai ya hana ni, daga karshe na ce ai Idea ta ce ta kare. Daga baya da yake dole dai sai na ci gaba da rubutun Allah ya warware komai na dawo cikin harkar.

Takamaimai, wai yaushe kika fara wallafa littafi, kuma zuwa yanzu kin wallafa littattafai nawa?

Akalla yanzu shekaru Bakwai da fara wallafa littafaina. Na kuma rubuta littafai Tara na fitar da Bakwai kusan kamar duk shekara nake sakin Daya. Bakwan da na fitar su ne: Kowa Ya Kwana Lafiya, Ina Mu Ka Dosa? Sirri, Zuciya, Mafarin Lamari, A Karan Kaina, A Mafarkina.

To a cikin Bakwan da kika fitar wanne ne gagarabadau a cikin su?

(Dariya) AKARAN KAINA. Babu abinda zan cewa littafin sai san barka. Da farko muna tunanin SIRRI ne ya ciri tuta, sai da Akaran kaina ya fito, sannan ya doke duk wasu littafai da na yi. Littafin ya ba ni tsoro sosai. Domin littafin har yanzu yana kan ganiyarsa, babu alamun tauraron littafin zai disashe.  Kankat duniya suna ganin kamar na gama littafi kamar Akaran kaina, a ya yin da ni ma da farko nake tunanin kamar fasahata ta kare a littafin Akaran kaina, sai daga baya na fahimci ba haka bane.

 

To me za ki ce ga kamfanin MAIZAR da ya ba ki wannan kambu domin girmamawa da kuma karfafa gwiwa?

Idan na ce zan godewa kamfanin nan kamar ban biya su ba. Abu Daya na yarda na amince zan yi wanda zai sa Kamfanin su kasa danasanin mallaka min wannan kambu shi ne, in sake yunkurowa da karfina wajen yin littafan da za su sake daga martabar kamfanin.

To ko kina da wani sako ga makaranta littattaffanki da kuma yan uwanki marubuta?

Sakona ga makarantana, a kara hakuri da ni. Kowani dan adam yana da kuskure yana da dai-dai. Ban taba kin daukar wayarsu da gangan  ko girman kai kamar yadda wasun su suke fadi ba, a’a su dauka wannan ne hanyar da ban cika dari ba. Idan komai ya zo dai-dai za su ji ni yadda su ke so. Shawarata ga marubuta dangina kuma, su dage wajen gudanar da bincike kafin yin littafin su. Kamar Akaran kaina, littafin gabadaya bincike ne ya jawo masa wannan matsayin, domin ban dora biro ba, sai da na gudanar da bincike mai zurfi.

Hajiya Inteesar Ahmad, makaranciya ce da ta zabi Fatima Danbarno a matsayin gwanar ta da dukkan littattafanta ba sa wuce ta da zarar sun fito. Wakilinmu ya tambaye ta cewa: “Shin ko me yake burge ki a cikin rubutunta da har kika zabe ta a cikin gwanayenki?

Labarinta yana kayatarwa kuma yana jan me karatu har karshe ba kamar sauran littafai ba da kana fara karantawa kasan karshen sa. Kuma salon bayar da labarinta ma daban ne da na sauran marubuta.

To me za ki ce game da AWARD din da ta samu?

Ta chanchanta gaskiya saboda littafan ta suna kunshe da duk wani abu na wannan yanayin rayuwar da muke ciki ba wai soyayya kadai ba.

Kasancewar dan adam tara yake bai cika Goma ba, ko kina ga a rubutunta akwai wani gyara da ya kamata ta yi?

Gyara guda Daya ne ta daina jan rubutu zuwa 4 a bar shi a 2 kawai duba da yanayin rayuwar da muke ciki.

To bayan haka ko kina da wata shawara  ga sauran marubuta gaba daya?

Shawara dai Daya ce ga sauran marubuta ita ce su chanja salo daga soyayya zuwa rayuwar mu ta yau da kullum.

To Hajiya Inteesar mun gode.

Ni ma na gode.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: