Dorin gida ko na gargajiya, na iya jawo mummunan lahani ga tsokoki, jijiyoyin jini, jijiyoyin laka, hadi da shi kansa kashi. Hakan na faruwa ne, sakamakon katsewar gudanawar jini sakamakon daurin dorin.
Lahani na fara faruwa ne daga awa uku zuwa shida bayan daurin da ya katse gudanawar jini a gaba da daurin.
Idan katsewar jini ta zarce, za ta iya haifar da ruvewar hannu ko kafa; wanda daga karshe zai tilasta yanke sashin a asibiti dungurungum.
- An Yi Wa Matashi Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Yarinya Fyade A Kebbi
- Rahoto : Kasar Sin Ta Samu Karuwar Baje Kolin Masana’antu Da Fasahohi A Shekarar 2024
Amma akwai alamomi biyar da za su iya taimakawa wajen gano katsewar gudanawar jini ta faru, sannan kuma hannu ko kafa su fara ruvewa.
Alamomin na fara bayyana ne, tun daga awanni ukun farko da suka hada da:
1- Matsanancin ciwo a inda aka yi daurin karayar.
2- Shanyewar hannu ko kafa: A yayin da jijiyoyin laka suka samu lahani, hannu ko kafa za su shanye; wato rashin kwari zai bayyana, sannan mutum ya gaza motsa yatsun hannun nasa ko na kafarsa.
3- Gushewar ji a fata: Idan aka tava hannu ko kafar mutum, ba zai ji ba, ko kuma ya rika jin dindiris, sagewa, jin kamar shokin ko kuma kamar ana tsitstsira masa allura.
4- Kodewa: Hannu ko kafa za su kode ko kuma su dashe, hakan na nuni ga kamfar jini a sashen.
5- Daukewar bugawar zuciya: Akwai wasu sassa a jikin mutum da ake iya jin yadda zuciya ke bugo jini zuwa sassan jiki, wato ‘pulse’. A hannu, ana iya jin bugawar zuciya a kan gavar gwiwar hannu da kuma tsintsiyar hannu; daidai kasan babban yatsan hannu. Haka nan, ana iya jin kafa a kan tafin sawu.
Da zarar wadannan alamomi sun fara bayyana, sai a garzaya zuwa asibiti; domin ceto hannun ko kafa daga ruvewa. Amma idan har aka yi buris da faruwar hakan, daga karshe zai tilasta yanke hannun ko kafa a asibiti; wanda kuma yanke wani sashen jikin mutum, na nufin samun nakasa ne kai tsaye.