Allah Ya Yi Wa Mai Martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga, Rasuwa,
Za a yi Jana’izarsa yau lahadi da Misalin karfe 2:00 na rana a kofar fadar Sarkin da ke garin Bajoga, Jihar Gombe.
Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘Yan uwa da Iyalai da Jama’ar Masarautar Funakaye da Jihar Gombe da Nijeriya baki daya.
Muna kuma Addu’ar Allah ya Jikansa da rahama, yasa Aljannah makoma.
Mun sami sanarwar rasuwar daga masu taimakawa masarautar Funakaye a kafafen sadarwa na zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp