Connect with us

MAKALAR YAU

Almubazzaranci Da Gazawar ‘Yan Majalisar Tarayya A Majalisa Ta 7

Published

on

Cikin wani rahoto da aka buga a “Daily Post, June 3, 2015” game da rashin barkata komai da zaurukan majalisun biyu sukai, gami da almubazzaranci da ake da dukiyar al’umar kasa tsakanin Shekarar 2011 zuwa 2015, sun gabatar da wasu bayanai kamar haka;

“..Yawancin muhimman kudurorin doka da aka gabatar a zangon majalisar ta 7 (2011-2015) za a ga cewa bangaren zartarwa na gwamnati ne suka gabatarwa da zaurukan majalisun kasar: za a ga cewa wasu kudurori ne da suka danganci na kasafin kudi na kasa da na wanda zai bai wa gwamnati bangaren zartarwa ikon karbo bashi. Sai ya zamana zauren majalisun sun gajiya wajen samar da kudurorin doka masu dama wadanda za su taba rayuwar mutanen da suka taka gadon bayansu suka sami ikon zuwa majalisar a matsayin wakilansu..

.”

“.. Sai ya zamana duk da kasafin kudi na   naira miliyan dubu dari da hamsin (150) da ‘Yan Majalisun ke lankwamewa a duk Shekara, faro tun daga Shekarar da aka rantsar da su ta 2011, za a ga cewa da za a bai wa wannan majalisa ta 7 maki a kan mafi girman hakkin da ya rataya a kansu na “yin doka” bai fi su sha da  maki goma (10%) ba. A takaice dai, bai fi a ce zaurukan na samar da kudurin doka biyu kacal ne ba a duk Watan duniya…”

Waccan majalisa ta 7 da a baya aka ambata cewa da Hon. Kawu Sumaila da Sen. Kabiru Gaya duka suna zaman dirshan cikinta a wancan lokaci, wancan rahoto ya cigaba da fadin;

“…Cikin Shekaru hudu na zangon waccan majalisa, za a iske cewa majalisun sun amshi zunzurutun mazajen kudade har sama da kimamin Naira Miliyan Dubu Dari Shida (600b), wanda ya yi daidai da Dala Dubu Uku cifcif ($3) daga lalitar Kasafin Kudi na Kasa. Kusan za a iya cewa, cikin Kudurin Doka dari da takwas (108) da majalisun suka samar cikin Shekaru hudun, kudin ko wane kudirin doka guda (bill – 1) da  suka sami damar mai  da shi doka  ya tashi a naira miliyan dubu biyar da miliyan saba’in da biyu (5.72b)..

Na’am, ba za a hada balagar siyasar ‘Yan Majalisun Amurka da na Najeriya ba, amma saboda wani dalili na son zuciya gami da yin watanda da dukiyar al’umar Kasa, yakan bayu zuwa ga wajibcin yin kwatankwaci a tsakanin Majalisun Mabanbantan Kasashen biyu (Najeriya da Amurka).

 

Cikin Shekaru hudu (2011 – 2011) ‘Yan Majalisun Najeriya sun mai da Kudirin Doka (bill) zuwa Doka. Amma takwarorinsu na Amurka, sun  mayar da Bill dari shida da hudu (604) zuwa Doka cikin Shekara guda tal (1999). Har ila yau, a tsakanin Shekarar 2007 zuwa ta 2008, ‘Yan Majalisun Amurkan, sun yi nasarar mayar da Bill 460 zuwa doka.

Idan mai karatu zai ce ‘Yan Majalisun na Amurka sun fi namu kwarewa, saboda haka ba mamaki su fi namu saurin aiwatar da ayyuka cikin kankanin lokaci. Babu musu, dole a yarda da wannan hasashe na mai karatu. Sai dai ga wata “yar tambaya. Tun da kowa bai da ja cewa, na Amurka sun fi namu kwarewa da gabatar da zunzutun ayyukan majalisar, da za a ba ka ikon biyan mabanbantan ‘Yan Majalisun biyu albashinsu da sauran alawus – alawus nasu, don Allah kudaden su waye ya dace ya fi yawa cikinsu?.

Cikin wancan rahoto na Daily Post an fadi cewa, “..Kasar Amurka na biyan ‘Yan Majalisunsu Dala Dubu Dari da Saba’in da hudu ($174,000). Ita kuwa Kasar Ingila na biyan nata ‘Yan Majalisun Dala Dubu Dari da Biyar ($105,000). Su kuwa ‘Yan Majalisun na Najeriya na amsar Dala Miliyan Daya ne da Dubu Hamsin a Shekara ($1.050,000).

Daga cikin ababen da masu fashin – bakin suka gabatar, wadanda suke yi wa kallon ka iya jaza wa akasarin “Yan Majalisun wannan Kasa yin ADABO da kujerinsu a Zabe maizuwa na Shekarar 2019, akwai;

5-Abandoning Of Constituents;

-Yin Watsi Da Al’umomin Mazabunsu;

Ga yadda masu fashin – bakin suka ce, “..Bisa al’ada bayan shelanta wadanda suka sami nasarar lashe zabuka, wadanda suka sami nasarar kujerun na “Yan Majalisun Kasa, kan hada komatsansu ne daga ainihin matsugunansu ne zuwa babban birnin tarayya, Abuja, da zimmar kama aiki…”

“..Bayan sun tare a can Abujar, za a ga wasu cikin “Yan   Majalisun, kan cigaba da waiwayar jama’ar Mazabun nasu, ta hanyar ziyartar su a duk Satin duniya. Wasu kuwa kan kai ziyarar ne a wasu ayyanannun lokutan da duk Sati ba. Abin takaicin shi ne, wasu “Yan Majalisun, bayan an zabe su, to fa ba a sake ganin keyarsu, sai idan lokacin wani zaben ya matso. Wanda hakan ke bakantawa jama’ar mazabun nasu, tare da fassara irin wadancan “Yan Majalisu a matsayin wadanda suka ci moriyar ganga a karshe suka yasar da kwaurenta…”

Wadancan Masharhanta sun cigaba da cewa;

“..Daga farawar wannan Majalisa ta takwas a wannan Kasa zuwa yau, an samu wasu “Yan Majalisun da al’umominsu suka farmake su, sakamakon watsi da suka yi da su bayan lashe zabe. Wannan yanayi kadai, ya isa zama wata “yar – manuniya da za ta haska cewa lalle kam wasu masu kada kuri’a sun tanadi irin wadancan “Yan Majalisu a Zabe maizuwa na 2019”, yayinda za su sake rarrafowa   don neman kuri’ar jama’a “.

Tsokaci;

Yanzu haka a nan Kano da ma sauran sassan wannan  Kasa, irin wadancan “Yan  Majalisu na ta kwarara zuwa ga al’umomin mazabun nasu, sunai musu rabon MOTOCI da MAKUDAN KUDADE, alhali tsawon lokuta da suka gabata, sukan ga “Yan Majalisun ne kawai a Jarida ko a Talabijin suna barci a Zaurukan Majalisun na Kasa. Ko kuma su ji muryoyinsu a Gidajen Rediyo. Ko kuma su ji muryar HAMANONINSU. Ina nufin “Yan Barandansu dake fushi da fushin mayaudaran jagororin, maimakon yin fushi da fushin wadanda aka hau gadon bayansu aka sami kai wa bisa matsayin da Ragwagwen “Yan Majalisun suka sami kansu a kai.

Wani abin kaicon ma shi ne, sai aka wayi  garin cewa, a na fassara Dan Majalisa Nagari ko mai son Takarar Kujerar ne, da dimbin kyaututtukan da yake watsawa SHUGABANNIN JAM’IYYA da sauran DALEGET zuwa DATTAWAN BIRAI na Jam’iyya. Maganar dora wanda ke bisa kujerar ko mai neman kujerar bisa tsantsar SIKELI na ILMI, sai hakan ya zama wani kauyanci ko fassara mai irin wannan ra’ayi da ko dai MAHASSADI koko mai yunkurin hana – ruwa – gudu.

Abu na gaba da Masharhantan suka gabatar shi ne;

4-Battle For Gobernorship Seats;

-Dauki – ba – dadin Neman Kujerun Gwamnoni;

Masharhantan sun sun gabatar da bayanai kamar haka;

“..Da jimawa, wasu daga “Yan Majisun Wakilai da Sanatoci, kusan a kaikaice sun nuna muradinsu na darewa bisa kujerun GWAMNONIN JIHOHINSU. A na ma sa ran irin “Yan Majalisun dake da wancan ra’ayi, ba da jimawa ba za su shelantawa duniya wancan muradi nasu…”

“..Cikin “Yan Majalisun, akwai wadanda ke da burin gadar Gwamnonin nasu ne, saboda sun kammala zangonsu biyu da Tsarin Mulkin Kasa ya sahale musu. Sai dai wasu “Yan Majalisun, na da burin tunbuke Gwamnonin nasu daga karagar mulki ne ta – karfi, ko da ma zangon mulki guda ne suka yi..”

“..Tuni alamu sun jima da bayyana cewa, wasu “Yan Majalisun na Kasa tuni ne suka fara wasa addarsu don neman kujerun Gwamnonin nasu, a jihohi irinsu; Zamfara; Bauchi; Gombe; Kwara; Nassarawa; Niger; Kogi; Ogun; Osun; Oyo; Ekiti; Imo; Jigawa; Borno; Yobe; Taraba; Kaduna da sauransu ..”.

“..Irin wancan yanayi, na nusar da cewa irin wadancan “Yan Majalisu za su hadu da tsaikon komawa Zaurukan Majalisun. Ko da kuwa sun sami nasarar cimma muradun nasu ko akasin haka “.

(Za a cigaba In Sha Allah)

Advertisement

labarai