Connect with us

LABARAI

Al’ummar Ajikobi/Agbaji Sun Mara Wa Saraki Baya Kan Neman Shugabancin Kasa

Published

on

Shugabanin gundumomin Ajikobi da Agbaji da ke garin Illorin a jihar Kwara, a jiya Asabar ne suka ayyana goyon bayansu dari bisa dari wa muradin shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki na neman shugabancin kasar Nijeriya, suna masu bayyanasa a matsayin dansu.
Da suke bayani a hirarsu da ‘yan jarida a Illorin, jagororin gundumomin sun bayyana cewar sun amince da manufa da kuma tsarin shugabancin Saraki.
Wakilinmu ya labarto mana cewar a ranar Alhamis ne wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Omar Ayelabegan, ya fitar da wata sanarwa yana mai bayanin cewar basu gamsu da neman da shugabancin Saraki ke yi ba, yana zargi cewar mulkin Saraki bai amfanar da yankin da komai na ci gaba ba.
Da suke bayani wa ‘yan jaridan, jagoran gudunmar Ajikobi da Agbaji, Alhaji AbdulMuhmeen Tayo Moyosore ya shaida cewar ikirarin da Ayelabegan, da cewar babu wani tushe a ciki balle makama, yana mai bayanin cewar Saraki ya samar da ababen ci gaban jihar ta fuskoki daban-daban.
Alhaji Tayo ya bayyana cewar babu wani mazaunin yankin da zai ce Saraki bai samar da aiyukan ci gaba a wannan yankin ba illa mutum mai butulci, yana mai nuna cewar Bukola ya samar da muhimman aikace wadanda suka taba rayuwar talaka kai tsaye.
Ya ce; “Muna son sanar da illahin jama’an duniya kan cewar dukkanin jama’an Agbaji da Ajikobi suna nuna goyon bayansu ga dansu, shugaban majalisar dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ba za mu taba daina goyon bayansa ba. muna matukar alfahiri da samun Bukola Saraki, musamman kan aikace-aikacen ci gaba da raya yankin nan da ya samar, hadi da kwazon da ya yi wajen gina jihar Kwara, da kuma na mijin kokarinsa a wannan kujerar da ke kan na shugaban majalisar dattawa,” Inji su
“Mun riski lamarin da ke cewa Saraki ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe. Ba mu da shakka ko kokonton Saraki zai iya fitar da Nijeriya daga matsanancin yanayin da take ciki, muna da imanin cewar idan ya zama shugaban kasa zai kyautata Nijeriya a dukkanin matakai. Don haka mun amince mu mara masa baya dari bisa dari,” Inji shugaban yankin
Daga bisani ya bukaci illahin jama’an Nijeriya da su yi umumu su mara wa shugaban majalisar dattawa baya kan wannan muradin tasa na tsayawa takarar shugabancin kasa domin tabbatar da kai Nijeriya mataki na gaba.
Da yake tofa albarcin bakinsa, shugaban matasan gundumar Ajikobi na jam’iyyar PDP, Alhaji Yunus Abolakale, shi ma ya karyata zancen da ke cewa Saraki bai tabuka wa yankin komai ba, yana mai bayanin cewar matasa da daman gaske sun amfana gaya da shugabancin Saraki yana mai nuna cewar za su kuma ci gaba da mara masa baya domin ya kai ga gaci.
Ya nunar da aiyukan raya Agbaji da Ajikobi da shugaban majalisar dattawan ya samar, yana mai gode masa bisa hakan
Advertisement

labarai