Mamba mai wakiltar mazabar Chibok/Damboa/Gwoza, Ahmed Jaha, ya yi kira da a yi kokarin ganin an dawo da daukacin ‘yan Chibok da Boko Haram ta raba da gidajensu.
Jaha ya ce, duk da cewa Chibok da akasarin yankunan Borno a yanzu sun tsira daga ayyukan ‘yan tada kayar baya, amma da yawan mutanen da suka tsere daga jihar ba su dawo ba.
- Dalibar Chibok Da Ta Kubuta Daga Hannun Boko Haram Ta Samu Mijin Aure A Amurka
- Sojoji Sun Kubutar Da Wasu ‘Yan Matan Chibok 2 Bayan Shekara 9 A Hannun Boko Haram
Dan majalisar ya bayyana haka ne a yayin bikin al’adu na shekarar 2023 da shugabannin al’ummar garin Chibok suka shirya a Abuja, karkashin kungiyar raya yankin Kibaku (KADA).
Jaha ya ce, bayan kwashe sama da shekaru goma na gudun hijira, lokaci ya yi da mutanen za su koma gida.
Ya ce ’ya’yan da aka haifa a cikin wannan zamani da wadanda suka bar gidajensu tun suna kanana, suna bukatar su shiga cikin ‘yan umarsu da yada al’adun gidajen kakanninsu.
Ya ce dubban mutanen Chibok sun suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a sassan kasar nan da suka hada da Abuja.
A cewarsa, har yanzu ‘yan Chibok suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira kuma suna samun mafaka a Abuja da Legas da Kano da Fatakwal da Nasarawa da sauran jihohi.
Dan majalisar ya yabawa sojoji da gwamnatocin jahohi da na tarayya kan yadda aka dawo da zaman lafiya a galibin yankunan Borno da suka hada da Chibok.