Mutane uku ne suka mutu sannan sama da hekta 10,000 na gonakin shinkafa sun lalace sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.
Ambaliyar ruwan wadda ake kyautata zaton ta samo asali ne sakamakon bude madatsar ruwa ta wutar lantarki da ke Jebba, ta yi barna ga manoma da dama, tare da tafiya da amfanin gonakin da ake shirin girbewa.
- Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa MatuÆ™i Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – BulamaÂ
- Leicester City Ta Koma Gasar Yan Dagaji Bayan Shan Kashi A Hannun Liverpool
Shugaban kungiyar matasan Kede, Abdulrahman Abdulkadir Wuya-Kede ya ce, gonarsa ta shinkafa mai girman hekta uku na cikin wadanda abin ya shafa.
“Amfanin gonakin duka sun isa girbi. Wasu ma sun fara girbi lokacin da ambaliyar ruwa ta afku. Ba mu san dalilin da ya sa aka sako ruwan ba tare da sanarwar mutanenmu ba” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp