Ambaliyar ta yi barna a kananan hukumomi da dama sannan ta lalata gonaki da dama a Jihar Borno.
Yayin da ambaliyar ruwa ta ke ci gaba da barna a sassan Nijeriya, jihohin Borno da Yobe su ma ba su tsira ba, inda ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas a jihohin biyu.
- Dangote Ya Ceto Nijeriya Daga Durƙushewa – Odetola
- Ministan Ma’adanai Ya Bukaci Masu Harkar Ma’adanai A Jihar Nasarawa Su Zauna Lafiya
Daga cikin wadanda suka rasu har da kananan yara a jihohin Borno da Yobe, a sanadin ambaliya wadda ta lalata gonaki da dama da gidaje.
‘Yan uwan wadanda ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar rasa ransu a Jihar Borno, sun mika faruwan lamarin ga Allah.
A Jihar Yobe kuma, ambaliyar ta yi sanadin mutuwar yara kanana uku wadanda suka fita wasa ambaliyar ta cinye su a garin Nguru, a jihar.
Ambaliyar ruwan ta lalata hanyoyi da dama da suka hade jihar da wasu sassan jihohin Arewa.
Kazalika, ambaliyar ta kuma lalata gonaki, da rushe gidaje, a garuruwan da suka hada da Jumban, Nangere, Jakusko, Bursari Gashua Bade a jihar.
Ambaliyar ruwa dai a bana ta lalata gidaje, gonaki da kuma dukiya mai tarin yawa musamman a yankunan Arewa.