Sashin lura da lafiyar mata na likitancin fisiyo (physiotherapy), na da muhimmancin gaske ga masu juna biyu. Sakamakon bincike ya nuna cewa, masu juna biyun da suka halarci ajujuwan daukar atisaye yayin rainon ciki na samun garkuwa daga wasu matsalolin rainon cikin da haihuwa kamar haka:
1- Magance matsanancin ciwon baya da kuma kugu.
2- Rage hadarin kamuwa da ciwon siga yayin rainon ciki.
3- Rage hadarin kamuwa da hawan jini yayin rainon ciki, wanda alama ce daga cikin alamomin da ke nuni da hadarin samun jijjiga yayin haihuwa.
- Bankin Zenith Ya Tallafa Wa Matasa Da Naira Miliyan 77 A Jihar Legas
- Talauci Ya Sa Ake Samun Karuwar Matasa Masu Fasahar Waka A Nijeriya -Tiwa Sabage
4- Bunkasa aikin tsokokin kugu da ke taimaka wa uwa yayin nakuda, don samun haihuwa cikin sauki. Bunkasa aikin wadannan tsokoki zai rage hadarin kasa haihuwa da kai; wanda ka iya tilasta yin tiyata ko aiki; domin ciro da ko jaririn.
5- Rage hadarin samun matsalar kwacewar fitsara ko kuma kamuwa da cutar yoyan fitsari.
6- Rage hadarin budewar kugu- Matsala ce da kasusuwan kugu kan bude fiye da kima, sakamakon ballewar tantanin da ke rike da kasusuwan kugu yayin nakuda.
7- Magance matsalar kumburin kafa da kuma tafin sawu.
8- Magance matsalar kwacewar fitsari yayin da kuma bayan haihuwa.
9- Rage samun kiba ko teba fiye da kima yayin da kuma bayan haihuwa.
10- Rage damuwa da yawan bacin rai ko fushi.
11- Rage hadarin haihuwar bakwaini da dai sauran makamantansu.
Sai dai, atisayen yayin rainon ciki na bukatar tantance mai juna biyu kafin ta fara atisayen. Saboda haka, zai fi kyau a yi atisayen karkashin kulawar likitan fisiyo; domin samun damar wanyewa lafiya.
Tuntubi likitan fisiyo a dukkanin asibitocin da ke da sashin fisiyo (physiotherapy), domin fara daukar atisayen rainon cikin; don samun alfanun da aka ambata a sama.