ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Man Kwakwa Guda 12

by Sulaiman and Bilkisu Tijjani
4 months ago
Man kwakwa

Haka zalika, man kwakwa na maganin kurajen fuska, musamman ga maza dake yawan yin kurajen fuska, sakamakon gyaran fuska, idan su ka yi amfani da man kwakwa, in sha Allahu za su samu afuwar kurajen fuska

Baya ga kurajen aski, hakanan, man kwakwa na magance kurajen fuska da aka fi sani da finfus. Duk wanda ke fama da wannna matsala sai ya juri shafa man kwakwa a fuskarsa, da iznin Allah zai rabu da finfus.

2. Gyaran gashi:

ADVERTISEMENT

Man kwakwa wani sanadari ne da ya yi suna wajen maganin amosanin kai, kamar yadda mu ka rubuta tun da farko a sama, sannan ya na hana bushewa da karyewar gashi, sakamakon haka kuma sai ya samarwa da mace yalwataccen gashi mai sheki da tsayi.

3. Maganin Fason Kafa:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

Man kwakwa ya na maganin faso, ga mai fama da wannan matsala sai ya samu man kwakwa ya zuba gishiri ciki amma ba mai yawa ba ya gauraya su, ya ringa shafawa a kafar,  sannu a hankali zai ga bushasshiyar fatar na barewa da kanta, sannan kafar za tayi laushi, yadda za ta daina fashewa.

4.  Samar da Kuzari Ga Jiki:

Ga mutanen da ke kukan nauyin jiki ko kasala sakamakon yawan maiko a jikinsu, sai mu ce, albishir gare su. Yin amfani da man kwakwa zai magance musu wannan matsala cikin sauri. Koda yake, ana ganin man kwakwa a matsayin mai dake kunshe da maiko, sai dai masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, shi maikonsa ba mai lahani ga jiki ba ne, saboda haka ne ma  ya ke taimaka wa wajen narkewa da kuma fitar da duk wani maiko da ke da lahani ga jikin mutum, hakan sai ya haifarwa da mutum samun kuzari da walwala.

Mu hadu a sati na gaba

Idan mutum na son amfanuwa da wannan fa’ida ta man kwakwa, sai ya ke zuba man kwakwar cikin abinci ko cikin lemon don samun karin kuzari da karfi ga jikinsa.

5. Inganta garkuwar jikin dan Adam:

Man kwakwa na kara inganta garkuwa jikin dan Adam sakamakon yana kunshe da sanadarai irin su, lauric acid, capric acid da caprylic acid.  Bincike ya nuna wadannan sinadarai na matukar taimaka wa wajen bunkasa garkuwar jikinmu, hakan kuma na kare jiki daga kamuwa da kwayoyin cututtuka da ke haddasa wa mutum rashin lafiya.

6. Saurin narkar da  abinci:

Wani lokacin mutane kan yi fama da murdawar ciki sakamakon cushewar ciki wanda rashin narkewar abinci kan haddasa, bincike da! masana a fannin kiwon lafiya su ka gudanar ya nuna yadda man kwakwa ke tasiri kan wannan matsala ta rashin narkewar abinci.Don haka duk mai fama da matsalar sai ya yi amfani da man kwakwa don samun waraka.

7.  Inganta lafiyar hakori:

Man kwakwa ya shahara wajen kara karfi da lafiyar hakori, sannan ya na kare mutum daga kamuwa da cututtukan da kan shafi hakori da kuma dasashi. Dalili kuwa shine man kwakwa na kunshe da wasu sanadarai na ‘Calcium’ da ke da tasiri wajen wannan aiki.

Baya ga karin karfi da kuma kariya ga hakora, haka zalika, man kwakwa na sanya hakora su yi haske da fari. Idan ana son samun wannan fa’ida, sai a hada man goge hakori da shi. Yadda mutum zai hada man kuwa shine, zai hada man Kwakwa da ‘Baking Soda’ ya gauraya su waje guda, ya samu ‘brush’ ya ke goge bakinsa da shi. Zai sha mamaki.

8. Saurin Gusar Da Kayan Kwalliya Daga Fuskar Mata:

Kowa ya san yadda mata kan yi amfani da kayan kwalliya a fuskarsu, kaamr hoda, jagira ko ‘eye shadow’  da sauran su. Wani lokacin gusar da su ta hanyar gogewa ko wanke wa kan bata lokaci, kuma hakan bai cika sanya kwalliyar ta fita fes ba. Don saurin gusar da kwalliya kuma cikin sauki, ki shafa man Kwakwa kadan a jikin auduga ko kyalle mai tsafta ki goge fuska da shi, sannan sai ki wanke fuskarki.

9. Hana Fashewar Lebe:

Ga wadanda lebansu ke  yawan fashewa sai su samu man kwakwa su ke shafawa a leban akai-akai, zai hana tsagewar leben ta hanyar hana shi bushewa. Idan mutum yana kyamar yin amfani da man kwakwa zallarsa, sai ya kwaba shi da wani man ya ke shafa wa.

10. Maganin Kwarkwata:

Magani ne da aka gwada kuma aka ga fa’idarsa. Idan kina fama da kwarkwata ki ringa shafa man kwakwa a kanki tun daga matsirar gashinki har zuwa ilahirin gashin baki daya. Hakanan za ki iya hada man kwakwar da ruwan kal ki ringa shafawa a kanki. Hakika za ki ga aiki da cikawa.

11. Maganin Mura:

Bincike ya tabatar da cewa, man kwakwa na maganin mura da kuma ciwon makogaro. Idan mutum na fama da mura ko kuma ciwon makogaro sai ya ringa zuba cokali 2 zuwa 3 na man kwakwa cikin ruwan shayi ya na sha, ko kuma ya ke zuba man kwakwa da man tafarnuwa cikin shayin ko ruwan zafi da ikon Allah zai samu sauki.

Man kwakwa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Man kwakwa
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

September 5, 2026
Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

August 29, 2026
Man kwakwa
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Farce

August 23, 2026
Next Post
2027: Masu Neman Takarar Gwamnan APC A Yobe Sun Gana Da Shettima Kan Rikicin Zaɓen Fidda Gwani

2027: Masu Neman Takarar Gwamnan APC A Yobe Sun Gana Da Shettima Kan Rikicin Zaɓen Fidda Gwani

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.