Yusuf Shuaibu" />

Amfanin Man Zaitun A Jikin Dan’adam

Shi dai zaitun itaciya ce mai albarka da kuma ba da cikakkiyar lafiya a jikin dan’adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abu ne mai daraja.
Wasu daga cikin aikin man zaitun a jikin dan’adam su hada da
Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus sauda ya cakuda ya sha safe da yamma. Ya sa mu kamar sati daya yana sha, in sha Allahu zai bari.
CIWON KAI: Duk mutumin da yake ciwon kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da rana da dare.
Ciwon Hakori: Duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganyen zaitun da ‘ya’yan habbatussauda ya saka su a cikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga.
Ciwon Hanta: Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da rana daya da dare.
Ciwon Dasashi: Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.
Ciwon Sukari: Duk mutumin da ya kamu da ciwon sukari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci.
Ciwon Asma: Duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turarawa.
Ciwon Koda: Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a rana.
Ciwon Baya: Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa a bayan.
Ciwon Rama: Duk mutumin da ya ga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku, in sha Allahu zai yi kiba.
Zazzabi Mai Zafi: Duk mutumin da ya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya, sannan yana karanta Ayatul kursiyyu sau 7, yana tofawa a cikin yana shafe jikinsa da shi.
Kyawun Fuska: Duk mutumin da yake so fuskarsa ta yi kyau, ta yi fari wanda ba zai cutadda shi ba, to ya dinga shafa man zaitun da man habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai yi mamakin yadda fuskarsa za ta koma.
Zubewar Gashi: Duk maccan da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi ta wanne kanta da shi, sannan bayan ya dan huce sai ta zuba man zaitun a hannunta, sai ta shafe kannata da shi gaba daya kullum.
Karancin Jini: Duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana.
Bayan Gida Mai Kauri: Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan-gida, wani ma sai ya yi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya tura shi a cikin duburarsa.
Ciwon Mara Ga Mata: Duk matar da take haila tana fama da ciwon mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, in sha Allahu duk lokacin da za ta yi haila ba zai mata ciwo ba.
Sanyin Kashi: Duk mutumin da kashinsa ya yi sanyi baya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma ya shafawa a wajan.
Kyawun Fata Da Laushinta: Duk mutumin da yake so fatarsa ta yi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa da shi bayan ya yi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa za ta koma.
Kurajen Karzuwa: Duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirba shi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa a wajan har ya warke.
Ciwon Kunne: Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun dana habbatussauda yana digawa a kunnansa.
Cutar Kyasfi: Duk mutumin da yake da kyasfi a jikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe, ya daka shi ya yi laushi sai ya hada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.
Shafar Aljanu: Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu ba sa son shi. Don haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da shi a kowane hali, in da hali ma ya mai da shi mansa na shafawa.
Ciwon Kakkare: Duk mutumin da ciwon kakkare ya sa me shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaba, sai a zuba man zaitun din a cikin lalle a gauraya, sannan a karanta (Ayatul Kursiyyu) sau 7, a tofa a ciki sannan sai a tofa a jikin wannan karkare.
Ciwan Nono: Duk matar da take fama da ciwan nono, to ana hada man zaitun da garinsa a barbada a kan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.
Ciwon Saifa: Duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma zuma farar saka ya sha.
Tsutsar Ciki: Duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su ya sha, wannan tsutsar za ta mutu.
Ciwon Hanji (Ulcer): Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin kumasari da ganyan zaitun mai laushi ya jika su ya dinga sha har sai ya warke.
Fitsarin Kwance: Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun dana habbatussauda a zuba a nono a dinga ba shi yana sha zai dai na.
Mutuwar Jiki (Kasala): Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zai ji karfin jikinsa.
Yawan Zazzabi: Duk mutumin da yake yawan yin zazzabi, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi da kuma zuma mara hadi ya dinga sha.
Ciwon Gabobi: Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo, to sai ya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gabobi.
Kwarkwata: Duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta bari sai rana ta take sai ta zuba wannan man a kanata ta bar shi ya yi kamar minti 20, sannan sai ta wanke.
TARI: Duk mutumin da ya kamu da kowani irin tari, to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da ‘yar citta da tsamiya da zuma, sai ya hada su guri daya ya cakuda ya dinga ci.
Majinar Kirji: Duk mutumin da yake yawan majinar kirji, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu safe da yamma.

Exit mobile version